Kungiyar kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS da wadansu kungiyoyi biyu da ba na gwamnati ba, sun bayar da tallafin dabbobi guda 150 ga marasa galihu a jihar Kebbi a wani mataki na ganin sun dogara da kawukansu.
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyoyin guda biyu sun hada da ‘Regional Agency for Agriculture and Food’ da kuma ‘Association for the Promotion of Livestock Breading’ a yankin Sahel da kuma Savannah na Afrika.
An bayar da tallafin ne a yankin Tullun Dabaga Bachaka, cikin tallafin harda buhu iri da ya kai kilogiram 500.
Da yake gabatar da jawabi a Sakatariyar karamar hukumar Arewa Dandi ta jihar Kebbi, a ranar Asabar, shugaban hukumar ECOWAS din, Jean-Cluade Brou ya ce sun bayar da wannan tallafin ne domin bunkasa walwalar wadanda suka amfana da tallafin.
Dr Mohammed Fouad, jami’in ECOWAS din mai lura da jihar Kebbi, shi ne ya wakilci Brou a lokacin bayar da tallafin. Ya tabbatar da cewa shirin tallafin na su suna yin shi ne domin bunkasa bangaren kiwo da kuma samar da abinci tare da bunkasa bangaren noman abinci mai gina jiki da kuma rage radadin talauci.
A na ta jawabin, Uwargidan gwamnan jihar Kebbi, Hajiya Aisha Atiku-Bagudu ta bayyana gamsuwarta da jindadinta da wannan tallafin na ECOWAS tare da hadin guiwar wadannan kungiyoyi masu zaman kansu guda biyu inda suka yi hadin guiwa da gwamnati wajen bayar da tallafin.
Kwamishinan lura da lafiyar dabbobi, Aminu Garba Dandiga shi ne ya wakilci Uwargidan gwamnan jihar, ya kara da cewa marasa galihun na bukatar gudummawa da tallafi domin bunkasa kyakkyawar alaka da zaman lafiya a tsakani.