Kungiyar Gwamnonin Arewa sun taya mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekara 64 a duniya sun kuma yaba masa akan gudunmawarsa ga yaki da jahilci da bunkasar ilimi a yankin Arewa.
Simon Lalong, shugaban kungiyar ya yi wannan yabon a sakon taya murnar cika shekara 64 a duniya da aka aika masa.
Sakon wanda sakatarensa na watsa labarai Dr Makut Macham ya sanya wan hannu aka kuma raba wa manema labarai a Jos ranar Litinin.