Hukumar tsaro ta DSS ta ce masu fafutikar yankin Biafra sun kashe mata jami’anta guda biyu a Emene da ke Jihar Inugu.
Hukumar ta tabbatar da hakan ne a cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin. Inda ta jaddada cewa an kai wa jami’anta din ne hari.
Sai dai ƙungiyar IPOB, ta musanta batun tana mai cewa mutum 21 aka kashe daga cikin ‘yan ƙungiyar.