Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta ba da lamunin fitar da Dala biliyan 3.1 domin ƙarasa aikin inganta harkokin gudanarwa a hukumar hana Fasa-ƙwauri ta (NCS).
Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Shamsuna Ahmed, ce ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan halartar zaman majalisar zartarwa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.
Ta ce maƙasudin hakan shi ne mayar da dukkan harkokin gudanarwa na hukumar Kwastam su koma amfani da fasahar zamani musamman ɓangaren sadarwa da tattara bayanai.
A cewarta, yarjejeniyar kwangilar aikin na tsawon shekara 20 kuɗaɗenta za su fito ne daga masu zuba jari da kuɗaɗen shiga da ake sa ran samu daga hukumar waɗanda sun kai Dala biliyan 176.
Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, a nasa jawabin, ya jaddada cewa babu ko sisin kobo da gwamnatin tarayya za ta fitar daga lalitarta wajen gudanar da aikin.