‘Yan sanda a jihar Katsina sun cafke mutane 140 bisa zargin aikata fyaɗe a faɗin Jihar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sunusi Buba ya ce an damƙe mutanen ne bisa zargin aikata fyaɗe sau 87 a watanni Afrilu zuwa Yuni a ƙananan hukumomin jihar guda 34.
Ya ce dukkaninsu an gurfanar da su a gaban kotu domin zama izina ga masu mummunar ɗabi’ar.
Sunusi Buba ya ce rundunar na aiki tare da shugabannin addini da sarakuna da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin bayan matsalar fyaɗe a jihar Katsina.
A don haka ya kuma roƙi ’yan jarida da ƙungiyoyin kare haƙƙin su yi aiki tare da ’yan sanda wurin yaƙar matsalar fyaɗe da cin zarafi.
Ya yaba da haɗin kan da ke tsakanin hukumomin tsaro a jihar wajen yaƙar manyan laifuka.
Sannan ya yi kira ga jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai da za su kai ga daƙile miyagun laifuka da samar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.