Jarumi Sharukhan dai shahararren jarumi ne da yake da masoya da yawa a sassa daban-daban na duniya kuma jarumi ne da yake bayar da gudun mawa a dunuyar Bollywood wato masana’antar fim ta ƙasar Indiya, kuma jarumi ne da duk mai bibiyar Indiya dama wanda baya bibiyar fina-finan Indiya da indai aka ambace shi to kowa ya sanshi tunda ana kiransa da global icon wato wanda sunansa ya ratsa kunnuwan al’umma.
Sannan kuma a fagen soyayya babu jarumin da a kafi sani idan ba Sharukhan ba inda ake ganin yafi kowanne jarumi iya soyayya a masana’antar Bollywood ta ƙasar Indiya, wannan dalili ma shine ya sanya jaridar www.dimokuradiyya.com.ng tagano cewar a masoyan Sharukhan na duniya to kashi 70 cikin 100 dukkaninsu mata ne tunda daman su sunfi rinjaya a inda soyayya take, ga babban misali, idan za’a tara mata kamar guda 10 masu bibiyar Indiya to guda 6 daga cikinsu magoya bayan Sharukhan ne.
Haka zalika ga dukkanin mai kallon fim ɗin Sharukhan yasan shi da jaruma Kajol sun bayar da gudun mawa wajen koyawa wasu mutanen soyayya, domin kuwa akwai abin da a yaren Hindi ake cewa:
1. Kajol aur Sharukhan ne hum ko pyaar dosti hai = wato Sharukhan da Kajol a cikin fina-finan su sun koyamana cewar soyayya abota ce.
2. Hum raaz me Kajol aur Sharukhan ke shadi hona chahta hai = Mu masu kallon Indiya munkasance a ko yaushe munason muga Kajol da Sharukhan sun zamo ma’aurata ma’ana sun auri juna.
3. Sannan akwai abin da akecewa Sharukhan da Kajol “Best On Screen Couple” wato waɗanda sukafi dacewa da juna amma a dunitar fim.
Tabbas idan akayi duba da shekarun baya za a ga cewar jarumi Sharukhan yayi sanyi ba kamar da ba, duba da cewar a shekarun baya yakanyi fim kusan kowacce shekara kuma fim mai ɗaukan hankali da tsuma zuciya, amma yanzu gashi an wayi gari yau kusan shekaru biyu kenan jarumin baiyi sabon fim ba kwata-kwata. Domin rabonsa da yayi sabon fim tun tun ɗin Hero, wanda daga shi baikuma yin fim ba.
Amma kuma magoya bayan jarumin har yanzu suna tsumayensa akan sabon fim da zaiyi amma kuma har yanzu bai furta cewar ga wani fim da zaiyi ba, sai dai ana danganta jarumin da yin wasu fina-finai guda 3 da zai taka rawa a cikinsu inda jin zaiyi fina-funan ya sanya magoya bayansa murna badan komai ba domin suna jira suga jarumin nasu yayi sabon fim ko sababbin fina-finai.
Ga jerin fina-finan da akesa ran jarumi Sharukhan zaiyi a nan gaba:
1. Akwai fim mai suna Pathan, wanda akesa ran zai fito tare da jaruma Deepika Padukone.
2. Akwai fim mai suna Atlee, kuma fim ɗin na kudancin Indiya ne wato Tamil inda akesa ran Sharukhan zaiyi abin da ake cewa double role, wato zai fito a mai fuska biyu, ɗaya a babban ɗan ta’adda, sannan ɗaya kuma a mai bincike.
3. Fim na uku shine fim ɗin fasihin mai bayar da unarnin nan wanda ya saba nishaɗantar da masu sauraro wato Rajkumar Hirani inda fim ne da zai nishaɗantar.
Haka zalika jaridar ta www.dimokuradiyya.com ta tattauna da wata masaniyar Indiya wadda take a jahar Jigawa wato Amina Muhammad Adam kuma ‘yar jarida ce a gidan rediyon Sawaba f.m dake Jigawa inda muka tattauna da ita shin ko meyasa Sharukhan yayi sanyi a dunuyar Bollywood?
“Eh to ni ina ganin abu guda biyu ne yasa jarumin yayi sanyi a halin yanzu
1. Yanzu kusan ba iya yayin yin fim ɗin soyayya akeyi ba duba da cewar idan akayi duba daga shekaru 6 zuwa yanzu anyi wasu fina-finai da suka gigita duniya a masana’antar Bollywood kuma ba ayi wata soyyyar azo a gani ba a cikinsu kuma manyan jarumai ne ake ganin cewar sunyi su wato fina-funan da jarumi Aamir Khan yayi na PK da Dangal wanda sun kafa tarihi na kawo kuɗaɗe sama da Crore 300 kowannensu. Haka shima fin ɗin Salman Khan mai suna Bajranghi Bhaijan kaga duk ba fina-funan soyayya bane amma sun kafa tarihi wajen kawo kuɗin da fim ɗin soyayya bai kawo ba kuma Sharukhan baiyi fim wanda ya kawo Crore 300 ba.
2. Tsufa ya fara zuwarwa jarumi Sharukhan shiyasa ya fara yin sanyi a duniyar fim, amma kuma har yanzu musamman a wajenmu mu mata indai za’ayi maganar Sharukhan idan muka tuna abubuwan da yakeyi na soyayya a fim har tsuma jikinmu yakeyi”.
Jarumi Sharukhan ya shiga masana’antar Bollywood sherar 1988 inda kuma yayi aure sannan shi da matarsa suna haifi ‘ya’ya guda 3, haka jarumin yayi fina-finan da baza a manta dasu a duniyar fina-finai ta Bollywood ba kamar Dulwale Dulhaniale Jayinge da Kuch Kuch Hota hai da Channai Express da Devdaz da Dilwale da Rabne Banadi Jordi dai sauransu.