Tun bayan ɓullar cutar Coronavirus data tsayar da komai bama iya harkokin aasanni ba a’a har sauran al’amuran yau da kullum na kusan kowacce ƙasa, sai dai za a iya cewa cutar tafi yaɗuwa a wasu sassan duniya kokuma a wasu nahiyoyin na duniya daga cikin nahiyoyin da ake dasu a duniya. Za a iya cewa cutar bata ragargaji nahiyar Afrika ba kamar yadda take ragargaza a nahiyar turai.
Ganin hakane ma yasa koda a kakar wasan data gabata aka sanya dokar fafata wasa batare da ‘yan kallo ba duba da cewar gasar Laliga da gasar ajin Firimiya ta Ingila da gasar Serea A da kuma gasar Bundes Liga an kammalasu batare da ‘yan kallo ba inda itakuma gasar French League 1 aka dakatar da ita. Haka Zalika gasar zakarun nahiyar turai da gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai an kammalasu batare da ‘yan kallo ba.
Haka ma a nan nahiyar Africa wasu gasannin na rukuni-rukuni an kammalasu batare da ‘yan Kallo ba, itakuwa gasar ajin Firimiya ta ƙasar nan wato NPFL an dakatar da gasar ne a mako na 25 inda aka yanke hukunci aka bayyana ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Plateau United a matsayin zakarar datalashe gasar, haka zalika aka bayyana ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Enyimba da Rivers United da Kano Pillars harma da zakarar gasar wato Plateau United a matsayin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan dazasu wakilci Najeriya a gasar zakarun nahiyar Africa da kuma gasar ajin ƙwararru ta nahiyar Africa.
Itama ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles zata fafata wasanninta guda biyu na sada zumunta batare da ‘yan kallo ba wato wasannin da zata fafata da ƙasashen Algeria da Tunisia inda zasu fafata wasannin guda biyu a ƙasar Austria wato can nahiyar nahiyar turai.
Sai dai an bayyana cewar Najeriya zata fafata wasannin batare da ‘yan kallo ba, wannan shine karo na biyu da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Super Eagles zata fafata wasa ba tare da ‘yan kallo ba, idan za a iya tunawa a ranar 17 ga watan Yuli na shekarar data gabata Super Eagles ta fafata da Senegal a can filin wasa na Isma’ila dake ƙasar Masar Wanda shine wasa karon farko data fafata ba tare da ‘yan kallo ba.
Sai dai ayanzu haka sakamakon za a fafata wasannin ba tare da ‘yan kallo ba hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar nan ta bayyana cewar za a haska wasannin a gidan telebijin domin ‘yan ƙasar Najeriya su kalli wasan kamar suna can ƙasar ta Austria.
Najeriya dai zata kara wasan farko da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Algeria a ranar Juma’a, sannan kuma zasu fafata wasa na biyu a ranar Talata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Tunisia, dukkanin wasannin guda biyu dai ya nuna cewar Najeriya zata fafata da ƙasashen da suke a nahiyar ta Afrika ne sai dai ita Najeriya tana Afrika ta yamma yayin da su kuma ƙasashen Algeria da Tunisia suke a arewacin Afrika.