A yunƙurin fafata wasannin sada zumunci da jerin ƙasashen duniya suke yunƙurin yi a wannan makon daza a shiga da kuma mako tsakiyar mako mai kamawa inda wasu ƙasashen kuma zasu fafata wasannin neman cancantar buga kofin nahiyarsu, haka zalika wasu ƙasashen kuma hutawa zasuyi batare da sun buga komai ba.
Daga cikin wasannin sada zumuncin da za’a fafata harda ƙasashen nahiyar Afrika inda suma zasu fafata wasannin na sada zumunci, daga cikin ƙasashen harda ƙasar Algeria wadda zata fafata wasa da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, dukkanin ƙasashen guda biyu sun fito ne daga nahiyar Afrika sai dai za a iya cewa ita Algeria ta fito ne daga arewacin Afrika inda itakuma Najeriya ta fito ne daga yammacin Afrika.
Tuni dai ita ƙasar Algeria ta sauka a ƙasar Austria domin buga wasan sada zumunci da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, ita dai Algeria a farko bada ita Najeriya ta shirya wasan na sada zumunci ba inda da zata fafata wasanne da ƙasar Ivory Coast, amma kwatsam sai Ivory Coast ta aikowa da hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Najeriya cewar ta janye daga buga wasan sada zumuncin.
Biyo bayan faruwar hakan ya sanya canza ƙasar ta Ivory Coast da ƙasar Algeria inda kuma da gaggawa Algeria ta amshi tayin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles tayinata na fafafa wasan sada zumuncin da zasu fafata a ranar Juma’a 9 ga watan Oktoba na shekarar 2020.
Suma ‘yan wasan na Super Eagles sun fara hallarar can ƙasar ta Austria tun a yammacin jiya Litinin kuma dukkanin wasannin guda biyu a ƙasar ta Austria za a bugasu wato wasannin da Super Eagles zatayi kenan. Sai dai akwai sababbin ‘yan wasa guda 6 da aka tafi dasu a tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Super Eagles inda anasaran zasu fafata wasannin.
Rabon da Najeriya da Algeria su kara wasa tun a wasan kusa dana ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika wanda Algeria ta lallasa Najeriya daci 2 da 1 inda kuma ƙasar ta Algeria ta lashe gasar ta kofin Afrika gasar da ƙasar Masar ta karɓi baƙunci.