Biyo bayan kammala shahararren fim ɗinnan mai suna Lal Singh wanda jarumai irinsu Aamir Khan da Kareena Kapooor da da sautan jarumai wanda da ita Kareena ta fito a matsayin matar Aamir Khan idan ta fito a mai suna Maneela Chaddha sannan shikuma mijin nata wato Aamir Khan ya fito a mai suna Laal Singh Chaddha.
Wannan fim dai kamfanin Aamir Khan ne ya gudanar dashi inda haziƙin maiba da umarni wato Advait Chandan yaba da umarni sannan kuma shi Aamir Khan ya jagoranci fin ɗin. Tuni aka fara shutin ɗin fim ɗin amma kuma sabo da cutar nan ta Coronavirus yasa aka dakatar kuma lokacin ana gaf da kammala fim ɗin.
Amma tun bayan da aka bayar da damar buɗe sinimu a India jarjman da basu kammala fina-finansu ba suka koma bakin daga ciki harda fim ɗin Laal Singh Chaddha wanda Kareena Kapor da Aamir Khan suka fito kuma ahalin yanzu sun kammala wannan fim.
Sai dai a jiya Alhamis da hamma ita Kareena Kapoor ta ziyarci Aamir Khan inda suka tattauna akan wannan fim nasu da suka kammala inda acikin hirar tasu har sukayi wani barkwanci lokacin da suke tattaunawa akan hakan. Inda bayan sunyi wannan zama sai Kareena ta saka hotonsu da Aamir Khan a shafin dandalin sada zumunta inda take cewa.
“Tabbas komai yayi farko zaiyi ƙarshe yanzu na kammala dukkanin aikina na cikin fim ɗinmu mai suna Laal Singh Chaddha duk da tarin matsalolin dana fuskanta musamman akan cutar Coronavirus duk da kasancewa ina da juna biyu amma kuma an kai ga gaci na kammala wannan fim namu”
Amma kuma cikin wasa da dariya jarumi Aamir Khan ya mayarmata da martani wanda hakan ya sanyata dariya da nishaɗi sosai inda yace.
Waye ya gayamiki an kammala fim ɗin Laal Singh Chaddha, ayanzu haka yana ina ta roƙon daraktan ya sake ƙirƙirarmana wasu sababbin sina-sinai dazamuyi dake wato don kinga kina da juna biyu shine zakice kin kammala aikinki ba”
Nan take jaruma Kareena Kapoor ta fashe da dariya sosai irin dariyar da kowa ya ganta yasan tana cikin nishaɗi sosai na yadda domin ta daɗe tana murmushi da dariya lokacin.
Anso a saki wannan fim ɗin a shekarar 2020 amma kuma sabo da cutar nan ta Covid 19 yasa aka fasa sakinsa inda sai a sabuwar shekarar 2021 za a sakeshi wato lokacin bikin kirsimeti wato 24 ga watan Disamba. Amma kuma daga ƙarshe jaruma Kareena Kapoor ta godewa daraktan wannan fim da kuma shi kansa jarumi Aamir Khan.
Shidai wannan fim dukkaninsa a ƙasar India aka yishi sannan kuma anyi amfani da yaren Hindi lokacin yin wannan fim.
Amma jaridar www.dimokuradiyya.com.ng ta tattauna da shahararriyar mai sharhi akan fina-finan indiya dama ita kanta masana’antar Bollywood ta ƙasar Indiya wato Amina Abdurrahaman Hasan dake unguwar Birget Gama a jahar Kano inda aka tambayeta game da yadda Kareena Kapoor da Aamir Khan suka tattauna harsukayi barkwanci a junansa akan wannan fim nasu maisuna Laal Singh Chaddha inda Amina race.
“Eh ni kaina danaga labarin saidana yi murmushi, amma kuma abin da yasa sukayi wannan barkwanci shine, shi kansa zuciyar labarin fim ɗin nasu maisuna Laal Singh Chaddha ai akan barkwanci ne shiyasa shima jarumi Aamir Khan yayimata barkwanci, shiyasa nake sanarwa da mutane duk mai son kallon barkwanci na nishaɗi to ya daure ya kalli wannan sabon fim ɗin a shekara maizuwa don batkwancin da sukayi na dabanne a wannan fim”.