Mai martaba sarkin Ile Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi yayi kira da a gaggauta amince ma kungiyar yan banga da tsaron gandun daji,lasisin fara aiki a matsayin masu tsaron rayuka da dukiyoyin Al’umma
Oba Enitan na Ile Ife ya yi wannan kira ne a lokacin da shugaban kungiyar yan banga da tsaron gandun daji ta Najeriya Nigerian Hunter And Forest Security Service Joshua Osatimehin ya kai masa ziyara a fadar sa dake Ile Ife
Jaridar Punch Newspaper ta ruwaito Oba Adeyeye na cewa tunda harkar tsaro na neman fin karfin jami’an tsaron Najeriya lokaci ya yi da ya kamata a bawa yan banga lasisin fara aiki a matsayin jami’an tsaro
KARANTA WANNANYanzu-Yanzu: Tinubu Ya Bar Jihar Legas Zuwa Birnin Tarayya Abuja
Duba da yadda suka bada gudunmawa a wajen tsaron gandun daji da kuma yakar yan Boko Haram ya kamata a saka su a cikin jerin jami’an tsaron Najeriya masu lasisi da zasu iya kare rayuka da dukiyoyin Al’umma
A jawabin godiya da shugaban kungiyar ta yan banga da tsaron gandun daji yayi ya bayyana cewar yazo Ile Ife ne domin neman tubarakin sarkin da kuma sanyawar albarka
Nazo wannan masarauta mai dumbin tarihi ne domin neman tubaraki da kuma sanyawar albarka ta Oba Enitan,kuma muna neman goyon bayanshi wajen tafiyar da aikinmu cikin natsuwa da kwanciyar hankali
Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi yayin da yake magana da yarbanci ya kara da cewar sarakunan gargajiya zasu yi zama a hukumance su yi shawarar abinda ya kamata dangane da saka yan banga a harkar tsaro
Bayan sunyi shawarar sai su aika ma shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya saka hannun abinda ya zama dokar kasa
A WANI LABARIN KUMAKamata Yayi A Yabawa NAHCON Ba Adinga Zaginta Ba-Al Makura
Kamata yayi a dinga yabon hukumar kula da jin dadin Alhazai ta Najeriya ba a koma gefe a dinga zaginsu akan laifin da ba suyi ba
Sakataren din din din na ma’aikatar kula da jin dadin Alhazai ta Jahar Nasarawa Mallam Idris Ahmed Al Makura yayi wannan kira a Saudiya