Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Fc dake buga gasar kwallon kafa ta Firimiya League ta kasar Ingila ta bayyana daukar dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Rb Leipzig Dominic Szobozsloi
Dominic dan asalin kasar Hungary yana taka leda a Rb Leipzig tun bayan zuwansa kungiyar daga Rb Salzburg ta kasar Norway a shekarar 2021
A kakar bana Dominic ya buga kwallaye 31 inda ya jefa kwallo 20 kuma ya taimaka aka jefa 21 a wasannin gasar Bundesliga
Liverpool kamar yada ta bayyana a shafinta na Twitter ta bayyana daukar dan wasan akan kudi yuro miliyan 60 inda zai shafe shekaru 5 yana taka Leda a Anfield
KARANTA NAN Najeriya Za Ta Fuskanci Matsalar Abinci Nan da Watanni 3 Masu Zuwa – Bafarawa
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool na neman kara karfafa yan wasan tsakiyarsu bayan tashin da manyan yan wasan kungiyar James Milner,Alex Oxlade Chamberlain da kuma Naby Keita suka yi
Tun farko Liverpool ta dauko dan wasan tsakiyar Brighton And Hove Albion kuma dan asalin kasar Ajantina Marc Allister wanda ya lashe gasar cin kocin Duniya wanda aka buga a kasar Qatar
Marc Allister ya taka rawar gani a gasar ta kofin Duniya da aka kammala a kasar Qatar wanda kasarsa ta Ajantina ta lashe
Bayan kammala gasar,Allister ya samu yabo daga masoya harkar kwallon kafa akan rawar da ya taka inda kungiyoyi da dama a Turai suka nuna sha’awar daukarsa kafin Liverpool ta samu damar daukar shi akan yuro miliyan 40
A WANI LABARIN KUMAA Baiwa Yan Banga Aikin Tsaron Najeriya-Ooni Na Ife
Mai martaba Ooni Na Ife kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Jahar Osun Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya bayyana cewar ya kamata a bawa yan banga lasisin zama jami’an tsaro a Najeriya
Ya kara da cewa duba da gudunmawar da kungiyar yan banga da tsaron gandun daji ta Najeriya ta yi wajen tsaron gandun daji da kakkabe yan Boko Haram da suka addabi yankin Arewa ta Gabas ya kamata suma a saka su a harkar tsaro domin taimakawa Jami’an tsaron Najeriya