By Abbas Yakubu Yaura
Rikicin sace-sacen mutane da kashe-kashen da ake yi a jihar Imo ya zama barazana ga ita kanta cibiyar Sarakunan Gargajiya.Misali, a ranar 14 ga watan Disamba, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken gargajiya na tsohuwar masarautar Umuezeala-Ama da ke karamar hukumar Ehime Mbano a jihar, Aloy Igwe.
Sannan a ranar 13 ga watan Disamba, an yi garkuwa da wasu sarakunan gargajiya biyu, Acho Ndukwe da Paul Ogbu daga al’ummar Ihube da ke karamar hukumar Okigwe tare da kona gidajensu. Yayin da aka ceto Ndukwe bayan sa’o’i 24, Eze Ogbu ya gamu da ajalinsa a lokacin da jami’an tsaro suka kai samame a wani wurin masu laifi a karamar hukumar Orlu.
A dai ranar 9 ga watan Disamba, jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an yi garkuwa da basaraken gargajiya na tsohuwar masarautar Mbutu dake karamar hukumar Aboh Mbaise, Damian Nwaigwe da takwaransa na tsohuwar masarautar Atta a karamar hukumar Njaba, Edwin Azike. Yayin da aka yi garkuwa da Azike aka jefar da gawarsa a dandalin kasuwa dake unguwarsu,sannan aka sako Nwaigwe bayan ya shafe kwanaki biyu a tsare.
A ranar 19 ga watan Nuwamba, an yi garkuwa da basaraken gargajiya na Achi Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli, Henry Madumere dake Iho a karamar hukumar Ikeduru a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa taron jama’a. An sako ma’aikacin wanda shine mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar, Eze Madumere, bayan shafe kwanaki shida a tsare.
Tun da farko a ranar 19 ga watan Oktoba, wasu ‘yan bindiga sun kai hari hedikwatar karamar hukumar Njaba dake Nnenasa inda suka bude wuta kan sarakunan gargajiya. Yayin da biyu suka mutu nan take, wasu biyu kuma sun shiga suma kuma an kai su asibiti inda aka farfado da su.
Shugabannin gargajiya na taka rawa mai amfani wajen yin sulhu tsakanin jama’a da jiha, da inganta martabar kasa, warware kananan rikice-rikice da samar da tsarin tsaro na hukumomi saboda yawa rashin isassun ofisoshin gwamnati.
Kuma a cikin tsarin masu ruwa da tsaki na yaki da rashin tsaro, suna taka rawar gani wajen tattara goyon bayan jama’a don kokarin samar da zaman lafiya kuma ana daukar cibiyoyinsu aiki don magance rikice-rikice, warwarewa da kuma rigakafin rikici.
Tsarin Tsaron Kasa na Najeriya na shekarar 2019, takardar aiki na ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA), ya bayyana cewa sarakunan gargajiya na da matukar muhimmanci ga hadin kan kasa da zaman lafiya yayin da suke aiki don kiyaye al’adu, dabi’u,da imani. Suna aiki a matsayin masu sanya ido na farko wajen magance rikice-rikicen jama’a ta yadda za su ci gaba da zaman lafiya a tsakanin al’ummarmu daban-daban.
Wadannan tashe-tashen hankula na sace-sacen mutane da kashe-kashe da sauran tashe-tashen hankula sun barke a yankin Kudu maso Gabas tare da kaddamar da kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) a watan Disambar shekarar 2020 da reshenta masu dauke da makamai,na gabas maso kudu (ESN).inda suka ce Munyi Allah wadai da wannan haramcin na cin zarafi, garkuwa da mutane da kashe sarakunan gargajiya.
Wannan lokaci ne da ya kamata ‘yan sanda da hukumar tsaro ta (DSS) su tashi tsaye wajen ganin sun dakile wannan wulakanci da rashin tunani da ake yi wa cibiyoyi da dabi’un mu na gargajiya.
Haka kuma yana da kyau gwamnonin yankin da kuma kungiyar ‘yan kabilar Igbo, Ohanaeze Nd’igbo su fito su yi magana kan wannan danyen aiki.
A cikin rikon kwarya, ya kamata a samar da karin tsaro ga sarakunan gargajiya, sannan duk ‘yan kasa da ke da muhimman bayanai kan wadanda suka aikata laifin ko kuma ‘yan bindigar da za su iya ba da irin wadannan bayanai ga amintattun jami’an jihar.
Kazalika sun ce ga iyalai da dangin sarakunan gargajiya da aka sace ko aka kashe, muna jajanta musu, ya zama wajibi ga daukacin ‘yan Nijeriya su tabbatar da cewa ba a sake yin shiru na al’ada, ruhi da muryoyin al’ada da hukumomin kowane sarakunan mu ba.