A rana mai kama ta yau ne a shekarar 2016 wato shekaru huɗu da suka gabata kenan a ranar 23 ga watan Oktoba aka fafata wasa mai zafi a gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila wasan daya bayar da mamaki tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea da Manchester United.
Wasan dai Manchester United bataji da kyau ba inda Chelsea ta ragargazata daci 4 nema inda Pedro ne ya fara jefa ƙwallon farko sannan Gary Cahill ya jefa ƙwallo ta 2, shima Eden Hazard baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen saka ƙwallo ta 3. Can an kusan tashi daga wasa shima N’Golo Kante ya jefa ƙwallo ta 4 wasan da akatashi Chelsea ta samu maki 3 da kuma ƙwallaye guda 4.
Chelsea dai na fama da rashin nasara a wannan kakar wasan ta bana haka zalika itama Manchester United tana cikin wannan matsala ta rashin nasara a sabuwar kakar wasan ta bana baya da maƙudan kuɗaɗe da kowacce ta kashe musamman ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea.
A wasan mako na 6 wato a ƙarshen makonnan Manchester United zata fafata da Chelsea a filin wasa na Old Trafford dake birnin na Manchester, sai dai kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa a cikinsu tana yunwar samun maki 3 a wasan.
A tsakiyar makonnan dai kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa a cikinsu ta fafata gasar zakarun nahiyar turai inda Manchester United ta lallsa Paris Saint Germain har gida daci 2 da 1 yayin da ita kuma Chelsea ta buga kunnen doki da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla.