Mai ba Amurka shawara kan harkokin tsaro, Jake Sullivan, ya tattauna da Janar Nikolay Patrushev, sakataren kwamitin tsaro na kasar Rasha, a wata ganawa ta farko tsakanin Washington da Moscow tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, in ji fadar White House.
Sullivan ya sake nanata adawar Amurka game da mamayewar da aka Rasha ta fara tun ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2022.
Inda kuma ya shaida wa Patrushev cewa “idan Rasha na da gaskiya kan harkokin diflomasiyya to Moscow ta daina kai hare-hare a birane da garuruwan Ukraine,” in ji sanarwar.