Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya gana da shugabannin kabilar Tigrai a karon farko tun bayan da bangarorin biyu suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya watanni uku da suka gabata. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Hotunan da kafafen yada labaran kasar Habasha suka fitar sun nuna Mista Ahmed da wasu jami’an gwamnati suna zaune tare da manyan ‘yan kabilar Tigrai, ciki har da kwamandan sojojin kasar, Janar Tadesse Worede.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC Za Ta Sake Gudanar Da Sabon Zaben Fidda Gwani A Wasu Mazabu Dake Taraba
An ba da rahoton cewa sun tattauna kan ci gaban da aka samu wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, da kuma batutuwan da ke bukatar kulawa na musamman.
Yarjejeniyar dai ta kawo karshen yakin basasar da aka shafe shekaru biyu ana gwabzawa a yankin arewacin kasar.
Rahotanni sun ce an gudanar da taron ne a wani wurin shakatawa da ke kudancin kasar ta Habasha.
A wani labari kuma, Mark Lawrenson Yayi Hasashen Sakamakon Wasannin Tottenham, Man City, Man Utd Da Arsenal
Tsohon dan wasan Liverpool, Mark Lawrenson, ya yi hasashen sakamakon wasannin mako na 22 na gasar Premier ta Ingila (EPL). Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Manchester United za ta kara da Crystal Palace a yammacin ranar Asabar a Old Trafford, yayin da Everton za ta karbi bakuncin Arsenal