Gabanin babban zaben 2023 da ke tafe, gwamnatin jihar Yobe ta hannun ma’aikatar kula da makarantun piramare da Sakandare ta jihar ta bayar da hutun kwanaki 18 ga daliban makarantun jihar.
Bayanin Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun daraktan kula da makarantu, Bukar Modu wadda ta kuma nuna cewa hutun ya kasance ne domin baiwa dalibai da malamai damar gudanar da harkokinsu na ‘yan kasa a zabe mai zuwa.
KU KARANTA: APC zata sake gudanar da zaben fidda gwani a wasu mazabun Taraba
Sanarwar Mai taken, “Hutun Jadawalin Makarantun Jihar Yobe da aka Amince da shi a zangon karatu na 2022-2023”, an amince da hutun kwanaki 18 kuma bisa ga wasikar an tsara shi ne daga 23 ga Fabrairu 2023 zuwa 13 ga Maris 2023.
Hutun na kwanaki 18 yana la’akari da nisan wasu dalibai, musamman daliban shirin dake makarantun kwana, dana jeka ka dawo.
“Duk da haka, kwanaki 10 daga cikin 18 da aka bayar za a rage daga hutun wa’adi na uku don haka hutun zai kasance kwanaki 8 kawai. Don dawo da kwanaki 10, ɗalibai za su yi hutu don hutu na uku daga Talata 15 ga Agusta maimakon Juma’a 4 ga Agusta 2023 kamar yadda aka tsara tun farko a Kalanda“, in ji sanarwar.
Daraktan Hukumar Kula da Makarantun a cikin wasikar ya gargadi daliban da su daina bari a yi amfani da su a matsayin ‘yan daba, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar Yobe ta himmatu wajen kyautata rayuwarsu kuma za ta ci gaba da samar da ilimi mai inganci.
A wani labarin kuma: A Karon Farko, Faraministan Habasha Ya Sa Labule Da Shugabannin Kabilar Tigrai
Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya gana da shugabannin kabilar Tigrai a karon farko tun bayan da bangarorin biyu suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya watanni uku da suka gabata. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Hotunan da kafafen yada labaran kasar Habasha suka fitar sun nuna Mista Ahmed da wasu jami’an gwamnati suna zaune tare da manyan ‘yan kabilar Tigrai, ciki har da kwamandan sojojin kasar, Janar Tadesse Worede.