Hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasar Uganda ta bayyana cewa a yau Talata ne kasar Uganda za ta fara aikin hakar rijiyar mai ta farko a yankin mai na Kingfisher. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Ana sa ran nan da shekarar 2025 za a hako farkon ganga biliyan 1.4 na mai daga rijiyoyin da ke yankin tsakiyar yammacin kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dogayen Layi Yayin Da Mazauna Kano Ke Gaggawa Domin Samun Sabbin Kudade
“A yau mun sake daukar wani mataki kuma mun matsa kaimi domin hako mai na farko tare da kaddamar da aikin hakar rijiyoyin raya kasa da samar da rijiyoyin mai na Kingfisher,” in ji Hukumar Kula da Man Fetur ta Uganda (PAU) a shafin Twitter.
Shugaba Yoweri Museveni ne zai jagoranci taron kaddamar da aikin.
Yankin mai albakatun mai na Kingfisher na karkashin kulawar kamfanin CNOOC na kasar Sin da zai yi aikin hakar man, yayin da rijiyar mai na Tilenga ta biyu ke gudanar da aikin karkashin kamfanin TotalEnergies na kasar Faransa.
A wani labari kuma, Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Osun
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Osun ta bayyana ranar Juma’a 27 ga watan Junairu, 2023, domin yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola ya shigar.
Sanarwar wacce ke kunshe a cikin wata takarda ta kotu mai dauke da kwanan watan 24 ga watan Janairu, 2023, mai dauke da sa hannun sakatariyar kotun, kuma jaridar DAILY POST ta samu a ranar Talata a Osogbo.