Kwanaki bakwai da Babban Bankin Kasa (CBN) ya cika domin tabbatar da ingancin tsoffin takardun Naira, an yi dogayen layuka a kewayen injinan ATM a cikin birnin Kano.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta lura da yadda mutane kusan 50 ne suka yi layi a wasu na’urorin cirar kudi ta ATM da ke bankuna a cikin birnin Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Majalisar Dattawa Ta Bukaci CBN Ya Tsawaita Wa’adin Tsoffin Kuɗi
Wakilinmu ya je bankunan kan titin Maiduguri, Murtala Muhammad way da kewayen Sabon Gari a safiyar ranar Talata.
Yayin da wasu bankunan ke da injinan ATM da ya kai 10, wasu na da injunan aiki daya ko biyu kacal, wanda hakan ya sa abokan ciniki ke kara samun lokaci a cikin layi.
A wasu dakunan banki, ana ci gaba da bayar da tsofaffin takardun kudi ga abokan cinikin da ke janyewa ta mai irhar kudi, yayin da wasu kwastomomi suka yi sa’a da samun sabbin takardun kudi.
Wani kwastoma da ya samu sabbin takardun kudi, Ibrahim Kinchi, ya koka da cewa ya iya ciro Naira 20,000 ne kawai saboda manufar CBN na kayyade kudin da za a cire.
“Na zo nan tun bakwai da kwata kuma na iya cirar Naira 20,000 ne kawai kuma bukatuna ya wuce haka a kullum. A gaskiya ban ji dadin hakan ba.”
Shima da yake magana, wani kwastoma, Haruna Idris Gama, ya ce, “Tun da safe na je Bankuna akalla takwas, a titin Bello road, amma da aka zo kaina sai kudin suka kare.
“Wani batu kuma shi ne, dogon layin, mutane sama da dari da injinan ba zasu oya ba. Ina so in je kasuwa, me zan yi yanzu?
A wani labarin kuma, Ku Yi wa Allah, Ku Kara Wa’adi Sauya Kudi — Gwamnan Arewa Ya Bukaci CBN
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya roki babban bankin Najeriya da ya kara wa’adin ranar 31 ga watan Junairu domin sauya tsofaffin takardun kudi. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Tun a ranar 26 ga watan Oktoban shekarar 2022 babban bankin kasar ya sanar da fitar sabbin takardun kudi na naira 200, da naira 500, da kuma naira 1,000, inda babban bankin Najeriya ya dage kan cewa ba za a kara wa’adin ba.