Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce a shekarar 2021 da za a shiga za ta yi yaki ne da tashin gwauron zabi da kayayyakin masarufi ke yi.
Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa; gwamnatinsa za ta sanya ido sosai akan tsadar farashin abinci a sabuwar shekara, inda ya bai wa Babban Bankin Nijeriya, CBN umurni da ka da su sake su bai wa masu shigo da abinci kudi.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin da ya gana da kwamitin shugaban kasa kan tattalin arziki a ranar Talata a gidan gwamnati dake Abuja, inda shugaba Buhari ya ce ya zuwa yanzu kalla jihohi bakwai ne a Nijeriya suke noman shinkafa, a don haka a cewarsa dole ne mu ci abin da muke noma wa.