Dan takarar gwamna na jam’iyyar, NNPP, Abba Yusuf Kabir ya lashe zaben kananan hukumomi takwas cikin goma sha biyu da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta saki ya zuwa yanzu, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Hakan ya kasance yayin da dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna ya lashe sauran kananan hukumomi hudu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: INEC ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Akwa Ibom
Jami’in dake jagorantar karbar sakamakon zaben da aka tattara a kananan hukumomin jihar, kuma shugaban jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Farfesa Ahmad Ibrahim ne ya tabbatar da sakamakon.
Sakamakon ya kuma nuna cewa babban daraktan yakin neman zaben NNPP kuma tsohon shugaban ma’aikatan gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Ali Makoda ya rasa karamar hukumarsa a hannun jam’iyyar APC.
Ga yadda Sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ya kasance:
Karamar Hukumar Rano: NNPP ta yi nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe: Farfesa Adamu Jibril Alhassan
Masu jefa kuri’a wadanda aka yiwa rijista: 85,893
Masu kada kuri’a: 36,780
Sakamako
APC: 17,090
NNPP: 18,040
PDP: 225
ADP: 80
Kuri’u Masu inganci : 35,899
Kuri’un da aka ki amincewa dasu: 439
Jimlar kuri’un da aka jefa: 36,338
An rushe zaben rumfunan zabe 4 da kuma jefa kuri’a fiye da kima.
Karamar HukumarRogo: NNPP ta yi nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe: Farfesa Shehu Usman
Wadanda aka yiwa rijistar Masu jefa kuri’a: 117,162
Masu kada kuri’a: 30,647
Sakamako
APC: 11,112
NNPP: 18,559
PDP: 124
ADP: 42
Kuri’u Masu inganci: 30,065
Wadanda aka ki amincewa da su: 336
Jimlar wadanda aka jefa: 30,401
An Soke zaben rumfunan zabe 36 a cikin unguwanni 5 saboda tashin hankali
Makoda LGA: APC ta yi nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe: Farfesa Nuradeen Magaji
Masu jefa kuri’a wadanda aka yiwa rijista: 75,487
Masu kada kuri’a: 31,601
Sakamako
APC: 15,006
NNPP: 13,956
PDP: 101
ADP: 83
Kuri’u Masu inganci: 29,383
Wadanda aka ƙi amincewa da su: 221
Jimlar kuri’un da aka kada: 29,604
An Soke zaben RAs 6 da 13 PUs
Lamarin ya shafi kuri’u – 7,176
Kunchi LGA: APC ta yi nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe: Farfesa Abdulmalik Awwal
Wadanda aka yiwa rijistar Masu jefa kuri’a: 62,928
Masu kada kuri’a: 25,306
Sakamako
APC: 13,215
NNPP: 10,674
PDP: 39
ADP: 62
Kuri’u Masu inganci: 24,385
Wadanda aka ƙi amincewa da su: 367
Jimlar kuri’a: 24,752
An Soke zaben a cikin RA 7 da 9 PUs lamarin ya shafi kuri’u 4,932
Wudil LGA: NNPP ta samu nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe: Farfesa Umar Sani
Wadanda aka yiwa rijistar Masu jefa kuri’a: 116,966
Masu kada kuri’a: 45,335
Sakamako
APC: 20,299
NNPP: 21,740
PDP: 118
ADP:
Kuri’u Masu inganci: 43,663
Wadanda aka ƙi amincewa da su: 770
Jimlar kuri’ar da aka kada: 44,433
An Soke zabe RAs 4 da suka ƙunshi PUs 5
kuri’un da abin ya shafa – 3971
Karaye LGA: NNPP ta yi nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe: Farfesa Abdullahi Arabi
Wadanda aka yiwa rijistar Masu jefa kuri’a: 85,557
Masu kada kuri’a: 32,172
Sakamako
APC: 14,515
NNPP: 15,838
PDP: 77
ADP: 63
Kuri’u Masu inganci: 30,912
Wadanda aka ƙi amincewa da su: 427
Jimlar kuri’ar da aka kada: 31,339
An Soke zaben rumfunan PUs 17
Lamarin ya shafi kuri’u 3,589
Minjibir LGA: NNPP ta samu nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe: Prof.
Masu jefa kuri’a wadanda aka yiwa rijista: 94,186
Masu kada kuri’a: 37,718
Sakamako
APC: 16,039
NNPP: 17,575
PDP: 189
ADP: 148
Kuri’u Masu inganci: 35,916
Wadanda aka ƙi amincewa da su: 991
Jimlar kuri’a: 36,907
Albasu LGA: NNPP ta samu nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe: Farfesa Tijjani Darma
Masu jefa kuri’a wadanda aka yiwa rijista: 101,038
Masu kada kuri’a: 38,305
Sakamako
APC: 16,959
NNPP: 19,952
PDP: 293
ADP: 55
Kuri’u Masu inganci: 37,376
Wadanda aka ƙi amincewa da su: 197
Jimlar kuri’u: 37,573
An soke a cikin RAs 4 da suka haɗa da PUs 10 saboda rushewa da kada kuri’a fiye da kima.
Tsanyawa LGA: APC ta yi nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe: Farfesa Ganiyu Shonubi
Masu jefa kuri’a wadanda aka yiwa rijista: 80,477
Masu kada kuri’a: 36,557
Sakamako
APC: 18,746
NNPP: 16,769
PDP: 71
ADP: 78
Kuri’u Masu inganci: 36,060
Wadanda aka ƙi amincewa da su: 436
Jimlar kuri’ar da aka kada: 36,496
An Soke zabe a cikin RAs 2 da suka shafi PUs 30
Gabasawa LGA: NNPP ta yi nasara
Jami’in Dawo da kayan zabe: Farfesa Ibrahim Hameed
Jimlar masu kada kuri’a wadanda aka yiwa rijista: 87,374
Masu kada kuri’a: 39,461
APC – 17,584
ADP – 91
NNPP – 19,507
PDP – 1,269
Jimlar ingantattun kuri’u: 38,935
Ƙuri’un da aka ƙi amincewa da su: 475
Jimlar kuri’u: 39,410
An Soke zaben cikin gundumomi 4 da suka ƙunshi PUs 5 tare da jimlar adadin PVCs da aka tattara 2,637 a Dalilin Tashin hankali.
Ajingi LGA: NNPP ta samu nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe: Farfesa Ibrahim Yusuf
Jimlar masu jefa kuri’ar wadanda aka yiwa rijista: 87,420
Masu kada kuri’a: 32,678
APC – 14,438
ADP – 306
NNPP – 15,422
PDP – 103
Jimlar ingantattun kuri’u: 31,437
Ƙuri’un da aka ƙi amincewa da su: 724
Jimlar kuri’un da aka kada: 32,161
An Soke zaben da ya ƙunshi PUs 8 a cikin unguwanni 5 tare da jimlar PVC da aka tattara 4,921.a Dalilai: Yawan jefa kuri’a fiye da kima da tashin hankali.
Shanono LGA: APC ta yi nasara
Jami’in tattara sakamakon zabe:
Masu jefa kuri’a wadanda aka yiwa rijista: 75,981
Masu kada kuri’a: 32,067
Sakamako
APC: 17,249
NNPP: 13,650
PDP: 272
ADP:
Kuri’u Masu inganci: 31,591
Wadanda aka ƙi amincewa da su: 451
Jimlar masu jefa kuri’a: 32,042
An Soke zaben da ya shafi RAs 2 da suka shafi PUs 2 saboda yawan jefa kuri’a da lalata kayan zabe
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda Sun Cafke Dan Majalisar Wakilai Bisa Yunkurin Bankawa Ofishin INEC Wuta a Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke Isyaku Ali Danja da wasu ‘yan mazabar Gezawa bisa zarginsa da jagorantar wata tawagar ‘yan daba domin su lalata cibiyar tattara sakamakon zabe ta kasa (INEC) da ke karamar hukumar Gezawa a jihar Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Husaini Muhammad Gummel ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, yayin da yake gabatar da wasu mutane kimanin 164 da aka kama bisa laifuka daban-daban na siyasa a yayin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki da aka kammala kwanan nan.