Hukumar Kula da Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa tace bata ɓoye kowa da aka samu a tuhumar da ake yi a zargin badaƙalar miyagun ƙwayoyi daya haɗa da DCP Abba Kyari dakataccen Shugaban Hukumar Kwararrun Ƴan sanda ta Ƙasa.
Wannan na zuwa ne a yayinda Hukumar tayi kira ga ƴan Najeriya dasu zama masu haƙuri akan tuhumar data ke yi, domin gano waɗanda suke bayan kilogaram 25 na hodar iblis da aka samu a Filin Jirgin Enugu.
Mai Magana da Yawun Hukumar, Femi Babafemi ya tabbatar da haka ga Jaridar Daily Trust yana mai cewa Hukumar bazata ɓoye kowa ba, duk girman shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Uzodinma: Babban Taron APC Na Ranar 26 Ga Watan Fabrairu Zai Iya Canzawa
A lokacin da aka tambaye shi akan ƙin ambatar sunan wasu jami’an NDLEA a tuhumar Abba Kyari, Babafemi yace Hukumar bazata ɓoye kowa ba.
“Wane irin ɓoye wa kake nufi akan lamarin da anyi nisa? Duk wanda aka samu zai fuskanci hukuncin doka. Kuma wannan shine matsayar Shugaban Hukumar NDLEA Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa.
“Muna kira ga ƴan Najeriya dasu baiwa Hukumar dama tayi aikin ta, kuma mai tabbatar wa ƴan Najeriya cewa duk abinda bincike ya nuna, za’a sanar da Al’umma, inji shi.
An lura dacewa, Hukumar a ranar Talata ta fara bincike akan DCP Abba Kyari akan sanya hannun sa akan shigo da ƙwaya daga Brazi- Habasha zuwa Najeriya da yawan ta yakai kilogaram 25, kuma Hukumar zata kammala binciken ta a ƙarshen wannan satin.
Babafemi baiyi magana ba akan tuhumar Abba Kyari, yana mai cewa “bincike na cigaba da gudana.”
Comments 1