- A yau litinin ne ake sa ran bude aikin matatar man fetur ta hamshakin dan kasuwar Afirka Aliko Dangote.
- Matatar man ta Dangote zata tace ganga 650,000 a kowace rana.
- Kazalika matatar zata tace akalla lita miliyan 38 na Man fetur, Kananzir da man jiragen sama a kullum.
A yau litinin ne ake sa ran bude aikin matatar man fetur ta Dangote, wani reshen kamfanin Dangote Industries Limited dake jihar Legas.
Daga cikin wadanda ake sa ran zuwan su wurin taron akwai shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda zai kaddamar da aikin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Wasu Matuka Jirgin Sama Sun Rasa Ransu A Wani Hatsarin Jirgi
“Kokarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na ganin Najeriya ta dogara da kanta wajen tace danyen mai a cikin gida domin ceton karancin kudin kasar waje da ake amfani da shi wajen shigo da man fetur daga kasashen waje ya samu karbuwa, ganin yadda matatar Dangote zata tace ganga 650,000 a kowace rana, wadda ita ce guda daya mafi girma a duniya.
Mai taimaka wa Buhari kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar 22 ga watan Mayu, 2023.
Matatar mai ta Dangote ta na nan ne a shiyyar cikin da babu iyaka da ke Ibeju-Lekki a Legas, kuma an kafa ta ne domin sarrafa man fetur daga nahiyar Afirka da Asiya da kuma Amurka, tare da kai rarar man fetur zuwa kasashen waje.
Kazalika zata tace akalla lita miliyan 38 na Man fetur, Kananzir da man jiragen sama na Najeriya a kullum.
Matatar da aka kafa domin tace ganga 650,000 na danyen mai a kowace rana na canza danyen mai zuwa nau’ikan amfani da albarkatun mai kamar dizal, man fetur, man jiragen sama da kananzir.
Shugabannin Afirka Biyar Da Ake Sa Ran Za Su Halarci Taron
Kasa da shugabannin Afirka biyar ne ake sa ran za su halarci bikin bude matatar mai ta Dangote ciki har da shugaba Buhari.
Sauran shugabannin da ake sa ran zuwan su sun hada da shugaban Togo, Gnassingbe Eyadéma; Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo; Shugaban kasar Senegal Macky Sall; Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum; da shugaban kasar Chadi, Mahamat Deby.
Sai dai kuma shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame zai gabatar da sakon fatan alheri a bikin.
Sauran da ake sa ran zuwan su sun hada da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da sauran manyan baki a fadin kasar nan.
A wani labarin kuma, Ku Rantse Da Al-Qur’ani Baku Saci Dukiyar Jama’a Ba – El-Rufa’i Ya Kalubalanci Tsoffin Gwamnonin Kaduna
Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna ya kalubalanci tsaffin gwamnonin jihar da su rantse da Al-Qur’ani cewa ba su taba satar kudin al’umma ba.
El-Rufa’i Yace zan iya rantsewa bai taba satar ko Kobo na kudin al’umma ba.
Na zama Gwamnan Kaduna gida daya ne dani kawai a kan titin Danja a Ungwan Sarki.