- Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna ya kalubalanci tsaffin gwamnonin jihar da su rantse da Al-Qur’ani cewa ba su taba satar kudin al’umma ba.
- El-Rufa’i Yace zan iya rantsewa bai taba satar ko Kobo na kudin al’umma ba.
- Na zama Gwamnan Kaduna gida daya ne dani kawai a kan titin Danja a Ungwan Sarki.
Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna ya kalubalanci tsaffin gwamnonin jihar da su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su taba satar kudin al’umma ba don gina gidaje a jihar da Dubai,Tribune Online ta rawaito.
Da yake magana da harshen Hausa a gidan radiyo na jiha KSMC, ya yi zargin cewa daya daga cikinsu ya gina wani katafaren gida a kan titin Jabi da kudaden jama’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari, Tinubu da Wasu Shugabannin Afirka 5 Sun Shirya Bude Matatar Man Dangote
Ya kuma kara da cewa, “Bari gwamnonin da suka shude su fuskanci al’ummar jihar Kaduna, su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su taba satar kudin gwamnati ba.
“Zan iya rantsewa ban taba satar ko Kobo a asusun gwamnati ba.”
El-Rufai, wanda ke mayar da martani kan sukar da ‘yan adawa ke yi wa wasu manufofinsa ya bayyana cewa, “Na yi farin ciki da abin da muka gani. Ayyukan da muka fara da ingancin za mu shafe shekaru muna jin dadin su.
“Ba irin hanyoyin da suka yi a baya ba ne, bayan damina biyu, hanyoyin za su lalace. Wadannan ayyuka da muke yi, muna yin su da inganci.
“Na ji dadin abin da na gani, domin a gare mu muna son mutane su shigo Kaduna su ga babu wata hanyar da ba ta dace ba a ko’ina.
“Muna so mu ga titin kwalta a kowace al’umma ta Kaduna da fitulun tituna mai amfani da hasken rana, irin na Kafanchan da Zariya da kuma kananan hukumomin mu.
“Wannan shi ne burinmu, amma irin mawuyacin halin da gwamnatinmu ta fuskanta, ba za mu iya yin duk abin da muka yi niyyar yi ba, sai da muka ci bashi kafin mu yi abin da muka yi.
“Ba mu karbi wannan rancen ba don mu gudu zuwa Dubai mu sayi gidaje ko mu je titin Jabi don gina katafaren gida domin mu yi barci mai kyau, ba haka muke ba.
“Na zama Gwamnan Kaduna gida daya ne dani kawai a kan titin Danja a Ungwan Sarki.
“Ban gina wani katafaren gida ba, bana bukata. Ban saci kudin kowa ba, ina kuma kalubalantar duk wanda yayi mulkin jihar nan da wanda yake kanyi da su fito su rantse da Alkur’ani cewa, a lokacin da suke mulkin jihar, ba su sace kobo na albarkatun Kaduna ba, wanda ba hakkinsu ba ne.
“Na rantse da Allah zan yi wannan rantsuwar. Don haka, ina kalubalantar su duka. Kowa ya fito ya fuskanci al’ummar jihar Kaduna ya ce musu bai saci kudinsu ba.
“Domin mun san su ’ya’yan Santa ne, ba ’ya’yan Dangote ba ne; mun san su a makaranta. A ina suka sami kuɗin gina waɗannan gidajen? Wane irin kasuwanci suke yi? Mun sani.
“Shirye-shiryenmu da abubuwan da suka gabata ba haka suke ba. Fahimtarmu ita ce, shugabanci amana ce daga Allah, kuma gare ku za ku tsaya a gaban Allah don yin hisabi.
“Sakamakon haka duk Naira da Kobo da muka samu, ko kudin shiga ko kasafi daga Abuja ko rance, na rantse da Allah mun yi amfani da shi wajen ci gaban al’ummarmu, ba mu dauka muka saka a aljihunmu ba. ko kuma a kai su su sayi gidaje a Dubai, ba ma bukatar hakan,” in ji El-Rufai.
Gwamna El-Rufa’i ya shawarci mutanen da babban dalilinsu na shiga harkokin siyasa shine arzuta kansu da su jajirce, inda ya bayyana cewa siyasa tana nufin masu wadatuwa ne da kuma sadaukar da kai ga jama’a.
A wani labarin kuma, Kada Ku Yanke Mani Hukunci Dai-Dai da Lokacin Da Ina Minista – Akpabio
Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su tantance shi a matsayin ministan harkokin raya yankin Neja Delta.
“Ba zan so a hukunta ni da nadin minista a Neja-Delta ba, wanda kowa ya san wuri ne mai matsala.”
Akpabio yace gwara ayi masa hukunci a matsayinsa na lauya, kwamishina na shekara shida da kuma gwamna na shekara takwas.