Daraktan ‘yan kasashen na Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Tinubu-Shettima, Prince Ade Omole, ya mayarwa kwamitin yakin neman zabe rarar Naira miliyan N2.4m.
Kudaden dai sun kasance ma’auni ne na asusun yakin neman zabe na naira miliyan N10m na farko da aka raba wa tawagar ‘yan kasashen waje kan tunkarar zaben shugaban kasa na 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Asiri Ya Tonu: Yadda Wani Dan Kasar Kenya Yayi Shigar Mata Don Buga Wasan Mata
Omole, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya kuma bayyana cewa, daraktan ya kuma gabatar da takardar kashe kudade mai shafuka takwas da ke nuna yadda aka kashe kudaden da kuma rahoton yakin neman zabe mai shafuka 22,kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto.
Da yake bayyana cewa an mika takardun ga mataimakin sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Christopher Tarka, daraktan ‘yan kasashen waje ya kara bayyana cewa takardun sun yi cikakken bayanin ayyukan da suka yi a lokacin yakin neman zabe da kuma shirye-shiryen zaben.
Omole ya ce, “Abu mai mahimmanci, hukumar kula da ‘yan kasashen waje ta samu naira miliyan N10m kacal a lokacin yakin neman zabe. An ware kudaden ne don sufurin mambobin daraktocin kasashen waje amma naira miliyan N7.6m kawai aka biya yayin da aka mayar da kudaden kamar haka.
Da yake mayar da martani, Tarka ya yaba wa Omole da tawagarsa saboda jajircewarsu, rikon amana, gaskiya, da kuma gudunmawar da suka bayar wajen nasarar Tinubu.
Tarka ya kara da cewa, “Kwamitocin yakin neman zabe yawanci ba su mayar da kudaden ba amma kuma, kun sake kunna hanyar. Wannan Darakta ya dauki Tinubu da tsarin ayyukan APC ga duniya kuma ya ba da gudummawar abubuwan tunawa da yawa na miliyoyin Naira daga ‘yan Najeriya a fadin duniya.”
A wani labarin kuma,Kebbi: Mun Shirya Tsaf Don Sake Gudanar Da Zaben Ranar Asabar – INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC), ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da sake zaben gwamna da na ‘yan majalisar kasa da na jiha cikin nasara a Kebbi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa INEC ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu domin sake gudanar da zabukan gwamnoni a jihohin Kebbi da Adamawa da kuma zaben ‘yan majalisar dokoki na kasa da na jihohi a fadin wasu jihohin kasar nan.