Abun baƙin cikine yadda Mutane basa iya fita neman abinci saboda matsalar tsaro — Hayab
Shugaban Gidauniyar Global Peace na Ƙasa (GPFN) Rabaran John Hayab yace Zaman Lafiya shine kaɗai magani ga Ƴan Najeriya domin su amfana da ɓangarori na rayuwa.
Ya bayyana rashin jindaɗi na yadda matsalar tsaro ta ragu a mafiya yawan sassan Ƙasar nan, amma mutane bazasu iya komawa su cigaba da neman abinda zasu sama bakin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Dakarfin Tsiya Dakarun Rasha Sun Kutsa Kai Cikin Tsakiyar Birnin Mariupol – Magajin Garin
Dayake jawabi a wani shiri da Gidauniyar ta shirya a Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jahar Niger Rabaran Hayab ya bayyana damuwa na yadda da yawan ƴan Najeriya bazasu iya fita lafiya ƙalau domin jin tsoron ƴan bindiga.
Rabaran Hayab yayi taro da dukkanin masu ruwa da tsaki da manufar ilmantar dasu akan mahimmancin zama da kowa cikin kwanciyar hankali, soyayyar juna, yana mai cewa mahimmancin shirin shine a samar da hanyoyi domin tunkarar maƙiyan dake kawo tsaiko ga zumunci da zaman lafiya.
A cewar sa “dole mutane su yi ƙoƙari su fahimci kan su, haɗa kai da kuma yaƙar duk wani mutum dake da nufin gadar masu da wani tarnaƙi.
Yayi kira ga ƴan Najeriya dasu jefar da bambance-bambance tare da zama ƴan uwan juna domin zaman lafiya da fahimta a tsakanin su, domin al’umma ingantacciya.