Kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara wa’adin daina karbar tsofaffin takardun naira a kasar nan.
Bukatar Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na kungiyar ACF reshen jihar Kano, Malam Bello Galadanci ya fitar a ranar Asabar din nan.
KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta fitar da jadawalin zaben fidda gwani na gwamnan Abia
Sanarwar ta ce wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da gwamnatin tarayya ta kayyade ya kusan dakile ayyukan zamantakewa da tattalin arziki a jihar Kano da kasa baki daya.
Ya kara da cewa kin karban tsoffin takardun naira a hada-hadar kasuwanci saboda fargabar rashin iya ajiye kudaden a bankunan kasuwanci yana janyo wa talakawa wahala.
A halin yanzu dai hakan ya kara wa talakawa wahala, domin har yau bankunan suna baiwa kwastomomin tsofaffin takardun Naira wadanda nan gaba kadan wa’adin amfani da su zai kare.
A wani labarin kuma: Karancin Man Fetur Na Kara Ta’azzara Al’umma A Birnim Tarayya Abuja Da Kewaye
Jama’a da masu ababen hawa a babban birnin tarayya da kewaye, na ci gaba da kokawa kan halin kuncin da ake fama da su, ganin yadda karancin man fetur yake kara ta’azzara.
Majiyar Jaridar DIMOKURADIYYA da ta sa ido a gidajen man a ranar Juma’a ya ruwaito cewa an ga dogayen layukan motoci a duk gidajen da ke da man fetur
Wadanda ke da man fetur din suna sayarwa akan Naira 195 kan kowace lita yayin da gidajen sayar da kayayyaki na NNPC Limited ke raba Naira 194 kan kowace lita.