Jam’iyyar PDP ta fitar da jadawalin ayyukan gudanar da sabon zaben fidda gwani na takarar gwamna a jihar Abia.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Hakan ya biyo bayan rasuwar dan takararta na Gwamna a zaben 2023, Farfesa Uchenna Eleazar Ikonne, a ranar Laraba.
Jam’iyyar a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a Abuja ranar Juma’a, ta ce matakin ya biyo bayan tanadin sashe na 33 na dokar zabe ta 2022, kwamitin ayyuka na kasa (NWC).
KARANTA HAKANAN Jami’an Yan Sanda Sun Kwace Ikon Sakatariyar Jam’iyyar PDP A Abia
Bisa jadawalin ayyukan da jam’iyyar ta fitar, an bayar da sanarwar ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a ranar Juma’a 27 ga watan Janairu.
Ya kuma kayyade sayar da fom din tsayawa takara daga ranar 27 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Janairu, inda aka kayyade ranar karshe don gabatar da fom din da aka riga aka siya a ranar 1 ga watan Fabrairu.
Za a gudanar da tantance masu neman takara a cewar jam’iyyar a ranar 2 ga watan Fabrairu da kuma neman daukaka kara a ranar 3 ga watan Fabrairu.
Ya bayyana cewa an ba wa sabbin masu neman takara damar shiga atisayen na yanzu tare da wadanda suka fafata a zaben fidda gwani na farko.
“An kuma shirya Majalisar jihar (Nadin Dan takarar Gwamna) a ranar 4 ga watan Fabrairu,” in ji shi.
Jam’iyyar ta shawarci daukacin shugabanninta, masu ruwa da tsaki, mambobinta da magoya bayanta na jihar Abia da su yi amfani da wannan sanarwar kamar yadda ya kamata. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Tsofaffin Kudin Naira: Atiku Ya Bukaci Da A Tsawaita Wa’adin Amfanin
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi kira da a kara wa’adin da babban bankin Kasa CBN ya sanya domin daina amfani tsofaffin takardun kudin Naira da ke yawo.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa babban bankin Kasa ya bayar da ranar 31 ga watan Junairu, 2023 a matsayin wa’adin daina amfani tsofaffin takardun kudin Naira yana mai dagewa cewa ba gudu ba ja da baya kan wa’adin.