Adadin wadanda suka mutu sakamakon harbin da aka yi a wurare da dama a jihar Colorado, wanda ya kawo karshe lokacin da aka harbe dan bindigar da kansa, ya kai biyar, in ji ‘yan sanda a jiya Talata.
An fara harbe-harbe da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Litinin, kuma ya barke a akalla wurare hudu daban-daban a garuruwan Denver da Lakewood, in ji ‘yan sanda wadanda da farko suka ce adadin wadanda suka mutu ya kai hudu.
An kashe mata biyu tare da raunata wani mutum a wuri na farko a Denver, in ji ‘yan sanda, tare da harbe wani mutum a wajen gidansa.
Dan bindigar ya yi tattaki zuwa Lakewood makwabciyarsa, inda ya harbe wani mutum a cikin dakin tattoo mai suna Lucky na 13 har lahira tare da raunata wani mutum.
Yin aiki da bayanan da aka tattara daga hare-haren da aka yi a baya, jami’an Lakewood sun sami damar gano maharin yayin da yake matsawa wasu wuraren.
Dan bindigar ya shiga wata cibiyar kasuwanci inda ya harbe wata ma’aikaciya har lahira, kamar yadda ‘yan sanda suka ce.
Daga nan sai ya ci karo da wani dan sanda a cibiyar kasuwanci inda ya umarce shi da ya jefar da makaminsa. A musayar wuta da aka yi, dan sandan ya samu rauni amma ya harbe wanda ake zargin.
‘Dan bindigar ya mutu ne a wurin” in ji kakakin ‘yan sandan Lakewood John Romero. Ya kuma kara da cewa Dan sandan ya yi “aiki mai kyau” amma za ta bukaci karin bincike.
Ba a san dalilin da ya sa wanda ya harbe shi ba, amma ‘yan sanda sun ce “bisa ga abin da muka sani, ya nuna cewa wanda ya aikata laifin yana kai hari ga tatattun mutane.”
‘Yan sanda sun kwato makamai biyu.
Rikicin bindiga dai babbar matsala ce a Amurka kuma masu fafutukar kame bindigogi sun ce matsalar ta samo asali ne sakamakon yawaitar bindigogi da kuma dokar da ba ta dace ba.
AFP