Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke a matsayin “rashin adalci”, inda ya sha alwashin kalubalantar hukuncin a kotun daukaka kara.
Da yake mayar da martani kan hukuncin kotun a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Rasheed Olawale ya fitar, Gwamna Adeleke ya caccaki matakin da aka dauka na kada kuri’a a kan Mr Oyetola, inda ya kira ta “fassarar rashin adalci da akasarin masu kada kuri’a”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Kotu ta kori Gwamnan Osun Adeleke
Yayin da yake kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, Gwamna Adeleke ya sha alwashin daukaka kara kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, inda ya dage cewa shi ne wanda ya cancanta ya lashe zaben da aka yi a ranar 16 ga watan Yuli.
“Ina kira ga mutanenmu da su kwantar da hankalinsu. Za mu daukaka kara kan hukuncin kuma muna da tabbacin za a yi adalci.
“Bari mutanenmu su kasance da tabbaci cewa za mu yi duk mai yiwuwa don ci gaba da wannan wa’adin da ake yabawa,” in ji Gwamna Adeleke.
A wani labarin kuma, Ganduje Da Malaman Addini Sun Bukaci CBN Ya Kara Wa’adin Tsoffin Kudin Naira
Gwamnatin jihar Kano da malaman addinin Islama na darikar Tijjaniyya, Qadiriyya, da Izala a jihar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kara wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da babban bankin Najeriya ya kayyade, na daina karbar tsofaffin takardun kudin naira.
Kiran ya biyo bayan kudurin taron da gwamnan jihar Kano Ganduje, da manyan jami’an gwamnati, da malaman addinin musulunci suka yi a gidan gwamnati ranar Alhamis.