Jamilu Collins na Kungiyar SC Padeborn 07, ya isa sansanin Super Eagles da ke Kamaru kwana guda gabanin wasansu na farko na rukuni a gasar cin kofin Afrika (AFCON).
Da zuwan Collins, adadin ‘yan wasa a sansanin ‘yan wasan Najeriya ya kai 27.
Akwai shakkun cewa dan wasan bazai shiga Cikin jerin Yan wasan farko da Nijeriya zata fafata da Masarawa ba a yau Talata.
Shima Dan wasan baya na kungiyar Venezia FC a kasar Italiya, Tyrone Ebuehi, ya shiga sansanin horaswar Super Eagles ne a ranar Asabar don baiwa Tawagar kwarin Gwauiwa a baya.
Har izuwa jiya Litinin Odion Ighalo ne kawai dan wasan da aka gayyata wanda bai isa sansanin Super Eagles ba.
Ighalo ya tabbata ba zai buga gasar ba saboda kungiyarsa ta Saudi Arabiya ta kasa sakinsa domin buga wasan kwallon kafa na Gida Najeriya.
An cire Victor Osihmen da Emmanuel Dennis daga kungiyar yayin da kungiyoyin su – Napoli da Watford – suka kasa sakin su zuwa a gasar.
‘Yan wasan gaba uku ne suka zura wa Super Eagles kwallayen a gasar AFCON amma yanzu kungiyar za ta nemi gwarzon Union Berlin Taiwo Awoniyi da Sadiq Umar na Almeria da Kelechi Iheanacho na Leicester City don jagorantar ta a wajen zura kwallaye.
Wasan farko na Najeriya za ta fafata ne da Masar, a yau Talata 11 ga watan Junairu 2022.