Mai tsaron ragar Masar Mohamed El-Shennawy na fuskantar tsaikon samun damar buga wasan kusa da na karshe da Kamaru mai masaukin baki a gasar AFCON ta 2021 mai gudana, in ji jaridar PUNCH Sports Extra.
Al Shenawy dai ya samu rauni ne a wasansu na zagaye na 16 da kasar Maroco, inda kuma Mohamed Abou Gabal ya maye gurbinsa.
Wakilinmu ya kuma gano cewa Mohamed El-Shennawy na fuskantar tsaikon samun damar buga wasan kusa da na karshe.
“Al Shenawy ba zai buga wasan kusa da na karshe ba amma Gabaski (Gabal) zai dawo atisaye ranar Talata,” in ji wani jami’in kungiyar Masar da ya shaida wa PUNCH Sports Extra.
“Babu wanda ya yi imanin Masar za ta kai matakin hudun karshe amma yanzu dole ne mu yi imani za mu iya kafa tarihi.”