By Abbas Yakubu Yaura
Jiragen saman Japan da kwale-kwale na neman ma’aikatan jirgin yaki guda biyu a ranar Talata a wani jirgin yakin da ake kyautata zaton ya fado bayan tashinsa kwana daya kafin hakan, in ji kakakin gwamnati.
An gano wani bangare na jirgin F-15, amma hukumomi na ci gaba da neman mutanen biyu da ke cikin jirgin, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Hirokazu Matsuno ya shaidawa manema labarai.
Jirgin wanda ke kan aikin horo ya bace daga radar jim kadan bayan tashinsa da yammacin ranar Litinin, in ji Matsuno.
Jirgin dai ya bace kimanin kilomita biyar (mil uku) ta yamma-arewa maso yamma na tashar jirgin saman Komatsu a tsakiyar yankin Ishikawa, kusa da Tekun Japan.
“A yayin da aka gano wani bangare na jikin jirgin yaki a yankin, ana kyautata zaton jirgin ya fado,” in ji Matsuno.
Kakakin ya ce ana kokarin gano ma’aikatan jirgin da suka bata, tare da jiragen sama da jiragen ruwa na rundunar kare kai da kuma jiragen da ke sintiri a gabar tekun suna binciken yankin.
Kawo yanzu dai ba a bayar da wani bayani kan hatsarin ba, kuma ma’aikatar tsaron kasar ba ta yi kokarin kakkabo jiragen F-15 ba sakamakon afkuwar lamarin.
Kasar Japan ta sha ganin hadurruka da suka shafi sojojinta a wasu lokuta, ciki har da na shekarar 2019 lokacin da wani jirgin sama mai saukar ungulu samfurin F-35A ya fada cikin teku bayan da matukin jirgin ya samu matsala.
Hadarin dai ya janyo cece-kuce don gano matukin jirgin da kuma sirrikan dake cikin jirgin.AFP