Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kebe kananan hukumomi biyu kowacce daga gundumomin sanatoci uku na jihar Kano domin gudanar da aikin tantance sanatoci ta hanyar amfani da BVAS.
Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Juma’a ta nuna cewa za a kammala atisayen da za a fara da karfe 9:00 na safe da karfe 2-00 na rana a yau Asabar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa an zabi kananan hukumomin Gwale da Kumbotso a Kano ta Tsakiya, Bichi da Dawakin Tofa a Kano ta Arewa yayin da Wudil da Rano aka zaba a Kano ta Kudu.
KU KARANTA KUMA INEC Ta Sanya Ranar Gudanar Da Zaben Gwaji A Kasar Nan
Sanarwar ta ce Gwale tana da unguwar Dorayi, Kumbotso tana da unguwar Na’ibawa, Bichi tana da unguwar Bichi, da Dawakin Tofa tana da unguwar Dawanau, sai Wudil tana da unguwar Wudil, Rano tana da unguwar Rano.
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa Ya ce rumfunan zabe sun hada da Gwale, Dorayi Karamaprimary School (I) da Dorayi Karami Primary School (II) sannan Kumbotso tana da Na;ibawa primary school (I) da Na’ibawa primary school (VII).
Haka kuma, Bichi tana da Hagagawa primary school (I) da Hagagawa primary school (II) yayinda Dawanau Cikin Gari (I) Bagadawa Saiji (II) (Transformer).
A Wudil, za a yi gwajin a makarantar firamare ta Unguwar Danya (I) da kuma firamaren Unguwar Danya (II) sai Kofar Fada (I) da KofarFada (II).
A Wani Labarin Kuma Zabtare Albashi: ASUU Ta Shirya Taron Gaggawa Na Majalisar Zartaswa
Majalisar zartaswar kungiyar malaman jami’o’i ta kasa na shirin ganawa nan ba da dadewa ba domin tattaunawa kan basukan albashin ma’aikata na watanni takwas.
Duk da cewa majalisar zartaswar kungiyar ta kasa ba ta yanke ranar taron ba, shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatar wa da jaridar PUNCH cewa nan ba da dadewa ba za a dauki ranar da za a sanar da jama’a.