By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 15 ne suka mutu a ranar Lahadin data gabata a wani hatsarin mota daya afku a hanyar Achilafiya zuwa Kankama a karamar hukumar Yankwashi dake jihar Jigawa.
Hatsarin wanda ya afku da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Lahadi, ya rutsa da wata nota kirar Golf Salon da kuma wata motar Golf Wagon.
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar hatsarin inda tace babu daya daga cikin mutanen dake cikin motocin biyu da suka tsira da rayukansu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Shisu Lawan Adam, a wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, yace: “Lamarin daya faru da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Lahadi, ya shafi wata mota kirar Golf Salon mai lambar Kano XA 361 BCH, wanda direban ta mai suna wani Ashura Sani mai shekaru 35 wanda ya fito daga Kauyen Fago karamar hukumar Sandamu ta jihar Katsina da wata motar Golf mai lamba. FST 276 CX (Lagos), wanda wani Bashir Ahmed mai shekaru 25 ke tuka ta wanda shi kuma ya fito daga kauyen Unguwar Tudu dake karamar hukumar Yan kwashi ta Jihar Jigawa.
Sannan yace hatsarin ya afku ne a lokacin da direban daya daga cikin motocin ya yi yunkurin kaucewa wani rami dake kan titin, wanda hakan ya sa aka rasa yadda za a yi,har sai da hatsarin ya afku sannan kuma motar ta kama wuta.
“Sakamakon hatsarin, Bashir Ahmed da wasu fasinjojin dake cikin motarsa sun kone kurmus a nan take ba a iya gane su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Ashiru Sani, dayan direba da fasinjoji goma sha biyu sun samu munanan raunuka kuma an garzaya da su cibiyar kula da lafiya matakin farko (PHC) dake Karkarna domin yi musu magani.
“Duk wadanda abin ya shafa sun mutu ne bayan an kwantar dasu kuma likitocin sun duba gawarwakinsu,” inji shi.inda ya kara da cewa ana gudanar da bincike akan lamarin.