Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa ta samu korafe-korafe 814 da suka keta hakkin bil’adama, Wanda da kuma sama da 500 a cikin su na mata ne a bana, a jihar Bauchi.
Ko’odinetan hukumar a jihar, Yatcit Susan Dala, ita ce ta bayyana hakan a ranar Litinin din nan yayin wani taron jama’a da kungiyar matasa da kungiyoyin raya kasa tare da hadin gwiwar hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) suka shirya a kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Bauchi.
“Ya zuwa wannan shekarar ta ranar 24 ga watan Nuwamba, mun samu jimillar cin zarafin bil’adama 814, daga cikinsu fiye da 500 na cin zarafin mata da maza kanane,” in ji shi.
A halin da ake ciki, uwargidan gwamnan jihar Sokoto, Dr. Mariya Tambuwal ta yi tayin tallafin naira miliyan hudu ga mutane 200 da lamarin ya rutsa da su na cin zarafin mata da kuma masu bukata ta musamman.
Misis Tambuwal ta ce ta dauki matakin ne domin rage musu radadin wahala.
Anashi bangaren wakilin UNICEF ya koka da yadda ake samun karuwar cin zarafin mata da kananan yara tare da yin kira da a hada karfi da karfe domin yakar matsalar.