By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 24 ne suka mutu bayan wata gobara data tashi a wani asibitin kula da lafiyar kwakwalwa dake wani gini na kasuwanci a birnin Osaka na kasar Japan a ranar Juma’a, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ce, ‘yan sanda sun yi la’akari da yiwuwar konewa.
Gobarar daj ta tashi ne da sanyin safiya kuma ta dauki tsawon rabin sa’a a hawa na hudu na asibitin, wanda kuma yafi bada kulawar lafiya baki daya.
An ga kone-konen ne a cikin asibitin ta firam ɗin taga da suka kone yayin da ma’aikatan kashe gobara suka sanya tarpaulin don toshe wurin ganin.
Kafar yada labarai ta NHK da wasu manyan kafafen yada labarai na Japan sun ce mutane 24 ne suka mutu, a cewar ‘yan sandan yankin, wadanda basu tabbatar da adadin mutanen ba.
A safiyar ranar Juma’a wani jami’in hukumar kashe gobara ta Osaka ya yi fargabar mutane 27 ne suka mutu a gobarar. A Japan, likita ne kawai zai iya tabbatar da mutuwar a hukumance.
“Hukumar kashe gobara ta karamar hukumar tana binciken musabbabin tashin gobarar. Na samu rahoton cewa ‘yan sandan Osaka na gudanar da bincike kan gobarar kamar yadda gwamnan yankin Hirofumi Yoshimura ya bayyana a shafin sa na Twitter.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kafofin yada labaran kasar Japan sun ce wani mutum mai shekaru 50 zuwa 60 ya yi zargin ya tarwatsa wani ruwa domin tada gobarar.
Firaminista Fumio Kishida ya yi “ta’aziyya ta gaske” ga wadanda abin ya shafa da kuma jajantawa wadanda suka jikkata a cikin lamarin.
Sannan yace “Dole ne mu kai ga kawo karshen wannan mummunan lamarin. Dole ne mu fayyace sanadin da kuma yadda abin ya faru. Kuma dole ne mu dauki matakan hana faruwar irin wannan abun anan gaba,” inji shi.
Motocin kashe gobara da dama ne suka garzaya zuwa wurin da gobarar ta tashi, wadda ta afku a wani wurin hada-hadar kasuwanci dake kusa da tashar jirgin kasa ta Kitashinchi a birnin dake yammacin kasar Japan.