Daga Abdullahi Kebbi
Wani jirgin ruwa dauke da mutane 350 ya kife a kogin Mai-Ndome dake jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.
Jirgin ya kife ne kilomita 10 kafin sauka inda zaije.
Jirgin yana dauke da mutane 350 inda akayi nasarar ceto rayukan Mutane 183, inda ake ci gaba da neman sauran 30 din a cikin Ruwa.
Sai dai mahukuntan kasar sun bayyana cewa ana ci gaba da neman sauran jikkunan Wadanda suka bata.