Akwai Abinda Tinubu yake Ɓoyewa dangane da Bayanan Karatunsa a Jami’ar Chicago – Hadimin Atiku
Mai baiwa tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar shawara kan harkokin yada labarai Paul Ibe ya ce shugaba Bola Ahmad Tinubu yana da wani abu da ya ke boyewa game da tarihinsa na karatu a Jami’ar Jihar Chicago.
Ibe ya bayyana haka ne a matsayin martani ga ƙudirin da Tinubu ya gabatar na kalubalantar gundumar Arewacin Illinois da ta umurci Jami’ar Jihar Chicago ta fitar da bayanan karatunsa cikin kwanaki biyu.
Hukuncin kotun ya biyo bayan karar da Atiku ya shigar da ke ƙalubalantar nasarar Tinubu a zaɓen Shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Sai dai shugaban a cikin buƙatar da lauyoyinsa suka shigar ya bayar da hujjar cewa mai shari’a ya kamata ya gabatar da rahoto kawai tare da ba da shawarar ga alkalan gundumomi a kan irin wannan lamari, maimakon bayar da umarni na karshe da kuma buƙatar yin biyayya cikin gaggawa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rashin kyakkyawan Shugabanci ne ya haifar da rashin tsaro a Najeriya – Peace Corp’s Commandant
Da yake mayar da martani a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a Ibe ya ce “Ya kamata a yanzu hatta makafi sun san cewa Tinubu na boye wani abu a cikin bayanansa a Jami’ar Jihar Chicago da ma sauran wurare.
Ina fatan duk abin da ya kasance ba zai kasance da wani yanki da zai ba ‘yan Najeriya ciwon zuciya ba, da daɗewa ‘yan Najeriya za su ga ainihin matsayin Atiku a kan tarihin Tinubu a CSU lokaci ne kawai.”
Atiku wanda ya tsaya takara a zaɓen Shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP a ranar 11 ga watan Yuli ya shigar da ƙara, yana neman samun karin bayani kan tarihin karatun Tinubu a Jami’ar Jihar Chikagy CSU.
Takardun da tsohon mataimakin Shugaban ƙasar ya nema ta hannun lauyansa Angela M. Liu sun hada da bayanan shigarsa da karbuwarsa a ranakun halartar jami’a da suka haɗa da lambobin yabo na digiri da karramawar da Tinubu ya samu a jami’ar da dai sauransu.
Tinubu da CSU duk ta hannun lauyoyinsu sun shigar da korafin amincewa da bukatar a karkashin dokokin sirri.