Dan takarar jam’iyyar Adawa ta PDP a zaben Fabarairun 2019 a Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya jaddada kiran hada kai tsakanin Musulmi da Kirista game da ayyukan kungiyar Boko Haram.
Atiku ya yi wannan kira ne sakamakon harin da kungiyar ta kai a daren ranar Lahadi, inda ta kashe kusan mutum 30 ta hanyar kona wasunsu a cikin motocin da suke kwance a kan hanyar shiga garin Maiduguri.
Shi ma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Alllah-wadai da harin.