Akwai dambarwa a mako mai zuwa idan an kammala wasannin sada zumunta da ƙasashen duniya suka fara fafatawa tun a ranar Larabar data gabata, haka zalika wasannin sunci gaba a ƙasashen makonnan sannan kuma a ranakun Litinin da Talata za a ci gaba da fafata wasannin, sai dai za a iya cewa can Kudancin Amurka wato Latin suna fafata wasannin neman cancantar buga gasar cin kofin duniya ne.
Hakan tasa dukkanin ‘yan wasa suka tafi domin bugawa ƙasashensu wasanni inda suka bar ƙungiyoyin ƙwallon da suke fafatawa wasanni. Sai dai kuma wata dambarwa ta kunno kai tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da kuma ɗan wasansu Dembele dangane da ci gaba da zamansa a ƙungiyar.
Inda Barcelona ta nemi cewar zatayi zama da wakilin ɗan wasa Dembele cewar kada asake bari ya tsawaita kwantaraginsa tare da Barcelona duba da cewar zata sanyashi a kasuwa a watan Janairu na sabuwar shekara mai kamawa ta 2021 inda akesaran za a sake buɗe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasa.
Dembele dai tun shekarar da yazo ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brussia Dortmund ta ƙasar Jamus a shekarar 2017 yake ta fama da rauni inda yaje jinya tafi sau biyar, kusan za a iya cewa Dembele baya iya buga wasan watanni biyu batare da yaji ciwo ba.
Shidai Dembele ya bugawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona wasanni 52 inda ya jefa ƙwallaye guda 12 kacal, sai dai kafin zuwansa Barcelona ya bugawa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suka haɗar da Rennes na ƙasar Faransa da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brussia Dortmund dake ƙasar Jamus.