A ranar Alhamis ne babban alkalin jihar Ekiti, Justice Adeyeye Oyewole, ya saki fursunoni 34 a gidan yari na Ado Ekiti.
Babban Alkalin da ya isa cibiyar gyaran hali ya leka wurin tare da yaba wa jami’an gidan gyaran halin na Ekiti bisa yadda suke kuka tsaftar muhalli.
Mai shari’a Adeyeye ya yi nazari sosai kan shari’o’in fursunoni 508 da ke zaman jiran shari’a a gidan yari tare da sakin 34 daga cikinsu.
Kwanturolan hukumar gyaran hali na kasa da ya samu wakilcin mataimakiyar kwanturola Atinaro Titus, ya yabawa babban alkalin jihar ta Ekiti bisa wannan karimcin da ya nuna, wanda yace zai taimaka matuka wajen kwantar da hankulan fursunonin da har yanzu basu samu ‘yancinsu ba. da kuma sake farfado da fatan su na alheri a nan gaba.
Ya kuma yi kira ga alkalan kotun da su yi amfani da hukuncin domin rage cunkoso a wurin.
Atinaro ya shawarci fursunonin da suka sami ‘yancinsu da su kasance masu bin doka da oda.
Wadanda suka halarta a wajen taron sun hada da alkalan babbar kotun jihar, alkalai, jami’in ACC Alagbe O.T da ke kula da gidan yarin Ado Ekiti.
A wani labari kuma na daban.
Daga Bacci Wani Dan Takara A Jam’iyar APC Ya Sheka Barzau
Wani dan takarar jam’iyyar APC, a majalisar dokokin jihar Kwara, na yankin Oke-Ode, Cif Oladipupo Ola-Peters ya rasu.
Ola-Peters, wanda har ya zuwa rasuwarsa, jigo a jam’iyyar APC daga gundumar Ilere ta karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, ya mutu ne a yayin da yake baccu da safiyar yau Alhamis a Legas.
Idan za’a iya tunawa cewa Ola-Peters na daya daga cikin masu neman tsayawa takara a zaben fidda gwani na majalisar wakilai mai cike da cece kuce.
Har zuwa lokacin da Ola-Peters ya mutu, ya kasance yana fatan zama dan takarar, domin a safiyar yau ba a yi amfani da zaben fidda gwanin ba ko kuma kai wa wata yarjejeniya ba wajen cimma matsayar wanda zai sami tikitin jam’iyyar a babban zaben kujerar majalisar wakilai na yankin a shekara mai zuwa.
A sakon ta’aziyyar da mai magana da yawun Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, Rafiu Ajakaye ya fitar a Ilorin a ranar Alhamis, ya bayyana rasuwar Ola-Peters a matsayin abin ban tsoro.
Ya jajantawa al’ummar Idera da ke karamar hukumar Ifelodun da kuma iyalan jam’iyyar APC bisa rasuwar fitaccen jigon jam’iyyar a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa, “A madadin gwamnati da al’ummar jihar, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalai tare da rokon Allah Madaukakin Sarki da ya hutar da shi, muna kuma jajantawa ‘yan uwa da duk wanda abun ya shafa”