Wata jarumai fim mai suna Oluwadarasimi Omoseyin, wacce tun da farko hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ICPC ta kama, yanzu haka hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC na binciken ta.
Jami’an ofishin hukumar EFCC na shiyyar Legas sun fara gudanar da bincike kan Omoseyin, da ta kware wajen gyaran fuska, bisa zargin yin sabatta juyatta da sabbin takardun kudin Naira.
KU KARANTA: Zanga-zanga kan karancin kudi na ci gaba da yaɗuwa
Hukumar EFCC a ranar Juma’a ta ce laifin ya sabawa sashe na 21 (5) na dokar babban bankin kasa CBN ta shekarar 2007.
Hukumar ICPC ta kama wadda ake zargin ne a ranar Laraba a kan titin Awolowo, Ikoyi, Legas, bayan wani rahoton sirri da ta samu.
An kama matashiyar mai shekaru 31 da haihuwa ne biyo bayan raba wani faifan bidiyo ta yanar gizo na watsi tare da taka sabbin takardun naira a wajen wani biki.
A cikin wannan faifan bidiyon, an ce an ga jarumar tana baje kolin sabbin takardun kudin Naira da aka sakewa fasalin.
Daga nan ne aka mika ta ga hukumar EFCC ranar Alhamis domin ci gaba da bincike.
Abubuwan da aka samu a tare da ita sun hada da Range Rover da wayar hannu ta iPhone.
Za a gurfanar da wadda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike, kamar yadda hukumar EFCC din tayi karin bayani.
A wani labarin kuma: CNG Ta Nemi CBN Ya Sauya Manufofin Musanya Kuɗi, Da Kayyade Fitar Da Kuɗin
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya, CNG, ta jaddada bukatar ta na gaggauta sauya tsarin takaita fitar da kudade na Babban Bankin Kasa (CBN) da kuma lokacin da za a yi musanyar tsofaffin takardun kudin Naira.
A wata sanarwa da mai magana da yawun CNG, Abdul-Azeez Suleiman ya fitar, ya ce ‘yan Najeriya ba za su iya lamuntar ” rashin kudi a hannun ba” ta Gwamnan CBN, Godwin Emefiele.