Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta ceto ragowar yara huɗu da aka sace a makarantar firamare ta Alwaza, ƙaramar hukumar Doma, ta jihar.
Yara shida aka sace a makarantar a ranar 20 ga watan Janairun 2023. Ƴan sanda sun ceto biyu daga ciki washegarin ranar da lamarin ya auku yayin da aka riƙe ragowar huɗun.
KU KARANTA KUMA: Abun tausayi: Bidiyon attajirin da ya samu lallurar taɓin hankali ya sosa zuciya
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar DSP Ramhan Nansel, shine a tabbatat da ceto ragowar yaran a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 3 ga watan Fabrairun 2023. Rahoton shafin Linda Ikeji ya tabbatar.
A cewar kakakin, an ceto yaran ne a ƙauyen Doka cikin ƙaramar hukumar Doma a ranar Juma’a, sannan za a miƙa su hannun iyayen su.
Sanarwar na cewa:
“A cigaba da ƙoƙarin ceto ragowar yaran makaranta huɗu da aka sace a ranar 20 ha watan Janairu 2023, a makarantar firamare ta Alwaza; a ranar 3 ga watan Fabrairu 2023, jami’an tsaro na haɗin guiwa tare da taimakon mafarauta sun ceto yaran a ƙauyen Doka cikin ƙaramar hukumar Doma.”
“Yaran masu suna Awazi Emmanuel, Success Ogah, Dominion Alhaji, da Success Emmanuel, an kai su asibiti domin duba lafiyar su inda daga nan za a miƙa su hannun iyayen su.”
Kakakin rundunar ƴan sandan yace kwamishinan ƴan sandan jihar, Maiyaki Baba, ya yabawa mutane bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin cewa an ceto yaran.
Wani magidanci Ya Cinnawa Matarsa Wuta Saboda Yi Masa Wanki Maimakon Bashi Abinci
A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun cafke wani magidanci bisa zargin babbake matarsa.
Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta cafke wani magidanci mai suna Hassan Azeez, mai shekara 46 a duniya bisa zargin kwarawa matar sa man fetur sannan ya cinna mata wuta.
Kakakin rundunar ƴan sanda jihar, SP Abimbola Oyeyemi itace ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar.