Al’ummar Nahuta a ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jahar Yobe, sun bayyana damuwa na yadda suka shafe watanni 6 babu wutar lantarki.
Wasu da suka yi jawabi ga Manema labaru a ranar Talata, sun ce lamarin ya haifar da taɓarɓarewar harkokin kasuwancin su a yankin, kuma rayuwa tayi ƙunci, a dukkanin lokuttan da aka shafe ba wutar lantarkin.
Malam Habu Abubakar wani daga cikin al’ummar yankin, yace sun kai rahoton lamarin na matsalar Na’urar dai-dai hasken wutar lantarki da take samar da wuta ta samu, a Hukumar kula da Samar da Hasken wutar lantarki ta Yola, amma har yanzu basu canja ta, ko kuma su gyara ta ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: IGP Ya Tura Sabon CP Ben Okoli Zuwa Jihar Bayelsa
Ya ƙara dacewa, a matsayin wani ƙoƙarin aikin gayya, Al’ummar yankin sun bada gudunmawar Naira dubu ɗari 450,000 domin gyara Na’urar dai-dai ta Hasken wutar lantarki, amma har yanzu basu gyara ba.
“An barmu cikin halin rashin wutar lantarki, kuma lamarin yana shafar harkokin tattalin arzikin Al’ummomin.
“Muna kira ga Gwamnati, da masu taimako, da wakilan yankin, dasu kawowa Al’ummar ɗauki ta hanyar Tallafawa Nahuta,” inji shi.
Garba Abdullahi wani mai aski a yankin, ya bayyana damuwa akan lamarin, inda yace lamarin ya shafi harkokin kasuwancin sa tun watan Afrilu 2021, wanda hakan ya sanya ya koma amfani da wata hanya domin yin harkokin kasuwancin sa da wahala da kuma tsada.
Duk ƙoƙarin da Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya tayi na ganim ta samu damar magana da Manajan Kamfanin Samar da Hasken wutar lantarki a Damaturu bai samu ba.