By Ishaq Dabai
Wata kotun Majistare dake Ikeja a ranar Talata ta bada umarnin garkame wani ma’aikacin gwamnati mai shekaru 29, Gabriel Awaye a gidan gyara hali saboda zargin lalata da karamar yarinya ‘yar shekara 13.
‘Yan sanda sun gurfanar da Awaye, wanda ke zaune a titin Agbawaye, Agbado Oke-Odo dake jihar Legas, da laifin lalata.
Alkalin kotun Majistare T.O. Tanimola, wanda bai karɓi roƙon Awaye ba na bada belinsa inda ta bada umarnin a cigaba da tsare shi a Cibiyar Kula da gyaran hali ta Kirikri.
Ms Tanimola, ta umarci jami’an ‘yan sanda dasu aika da karar zuwa ga Daraktan masu gabatar da kara na jihar (DPP) don neman shawara ta shari’a.sannan ta dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba don shawarar DPP.
Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, ASP Victor Eruada, ya shaidawa kotun cewa ma’aikacin ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Yuni, a gidansa.inda ya kara da cewa Awaye ya ja hankalin yarinyar zuwa cikin gidansa inda kuma yayi lalata da ita.
Eruada yace laifin ya sabawa sashe na 137 na dokar aikata manyan laifuka na jihar Legas na shekarar 2015.inda Sashen ya tsara ɗaurin rai da rai bisa aikata laifin lalata.