Dan majalisar mai wakiltar mazabar Rano, Bunkure da Kibiya a majalisar wakilai, Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya roki gwamnatin tarayya da ta jihar Kano da su gaggauta kai dauki ga dubban al’ummar da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu sakamakon ruwan dam din Tiga a Kano da ke barazana ga ayyukan noma da rayuwa al’ummar.
Jaridar Solacebase ta bayar da rahoton cewa daya daga cikin kafofin dam din na Tiga a ranar Alhamis din da ta gabata an ce ya mamaye gabar kogin zuwa filayen noma da gidaje da dama a yankin, saboda yawan ambaliyar da aka samu a kwanan nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Fatihu Yusif Bichi ya fitar, Rurum ya yi wannan kiran ne a wata ziyarar da ya kai yankin a ranar Asabar din nan sakamakon ambaliya da ruwan dam da ya shafi dubban jama’a a cikin al’umma da gonaki, da lalacewar hanyoyi tare da tilastawa kauyawan da ke kewaye da su guduwa zuwa tsira.
Karanta kuma: Akwai Yi Wuwar Kano Ta Fuskanci Wata Mabaliyar Ruwan
Sanarwar ta ce a yayin ziyarar, tsohon kakakin majalisar dokokin Kano ya ce bisa ga bayanan da ya samu daga wadanda abin ya shafa, sun yi zargin cewa hukumar kogin Hadejia da Jama’are ta yi lalata madatsar ruwan da aka yi a yankin, wanda daga baya ya yi barna akan al’ummar yankin.
“Sakamakon kwararar ruwan dam da ya haifar da ambaliya, dubban mazauna yankunan sun rasa matsugunansu,” in ji Rurum.
Har ila yau, da yake zantawa da Solacebase, Alhassan Rurum, ya ce ya tattauna da manajan daraktan hukumar kula da kogin Hadejia da Jama’are, domin tsara hanyoyin da za a hana afkuwar lamarin.
Ya yi alkawarin gabatar da batun a zauren majalisar wakilai domin gudanar da bincike da kuma rage radadin barnar da aka samu.
A wani labarin kuma: Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su, sun kwato makamai da alburusai da kuma motocin aiki a wurare daban-daban guda biyu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadin nan a Kaduna.