Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin cewa bisa la’akari da yadda aka samu ruwan sama da kuma adadin ruwan sama da aka samu a cikin watan Agusta, Kano na iya fuskantar ambaliyar ruwa a watan Satumba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa hukumar ta yi wannan gargadin ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Muntari Ibrahim a ranar a wannan makon.
A cewar NiMet, “Yashi da kuma ruwan sama mai yawa da aka samu a watan Agusta na iya sanya mafi yawan wurare su fuskanci ambaliya da suka hada da manya, matsakaita, karama da ambaliyar ruwa a watan na Satumba.”
KARANTA ANAN: Gwamnan Neja Ya Bayar Da Umarnin Gaggauta Rushe Wasu Gine Gine
NiMet ta kara da cewa wuraren da ke da manyan tashoshi na kogi na iya fuskantar babban hadarin aukuwar ambaliya saboda tarin ruwa da aka rigaya a kan magudanan ruwa wanda ba zai iya dauke wani karin ruwa ba.
NiMet ta shawarci Hukumomin Ba da Agajin Gaggawa na Jihohi su kara inganta hanyoyin daidaitawa, sassautawa da kuma mayar da martani yayin da ake shawartar jihohin da ake sa ran za su fuskanci matsalolin ambaliyar ruwa da su fara gangamin wayar da kan jama’a ta hanyar ma’aikatan fadada filayen don yuwuwar ayyukan ambaliyar ruwa a cikin watan Satumba musamman ma wadanda ke a yankin wurare masu haɗari.
A wani labarin kuma: Cutar Gudawa Na Hallaka Yara Dubu 124 A Najeriya – Sadiya Farouq
Akalla yara ‘yan kasa da shekaru biyar 124,000 ne ke mutuwa duk shekara a Najeriya sakamakon cutar gudawa da wasu cututtuka masu alaka da kamuwa da cutar bayan gida.
Ministar harkokin jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban jama’a, Hajiya Sadiya Farouk, ta bayyana hakan a lokacin da ta kai ziyara sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi da ke jihar Kuros Riba.