A yau juma’a ce Hukumar bada agajin gaggawa reshen jihar Kano SEMA, ta bayyana cewa, ambaliyan ruwa ya yi sanadiyar mutuwar Mutum 26 da kuma lalata gidaje 1,000 a kananan hukumomi hudu dake jihar, tun daga watan Afurilu shekarar nan zuwa yau.
Babban Sakataren Hukumar ta SEMA reshen jihar Kano Dr Sale Jili ne, ya tabbatar da wannan adadin, ga manema labarai a garin Kano, inda ya ce, Mutum hamsin sun sami mummunan raunika, sanadiyar ambaliyan ruwan.
A cewar shi, kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da, Bunkere, Minjibir, Tarauni da kuma karamar hukumar Doguwa da ke jihar.
Ya kara da cewa, tuni hukumar Kula da harsashen yanayi ta kasa Wato NiMet, ta yi hasashen samun ambaliyan, a wasu kananan hukumomi 25 dake jihar a wannan shekarar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mummunan zato mutane ke yi wa harkar Fim, inji Karima Izzar So
Sakataren ya ce, tuni hukumar ta ziyarci wuraren da lamarin ya shafa, domin jajanta mu su a madadin gwamnatin jihar, kuma ya ce, Hukumar ta raba kayayyakin tallafi, domin rage wadanda lamarin ya shafa ra’dadi.
” Kayayyakin da aka raba, sun hadar da buhunhunan siminti, Shinkafa, masara, alkama,da dai sauransu” a cewar shi.
Kazalika Sakataran hukumar ya kuma yaba wa Gwamnan Abdullahi Ganduje, da Kwamishinan aiyuka na musamman Mr Muntaru Ishaq, bisa irin tallafin da su ke bai wa hukumar.
Ya kuma yi kira ga wasu hukumomin da kuma masu ruwa da tsaki, da su tallafa wa wadanda lamarin ya shafa.
“Duba da yadda cutar COVID-19 ta karya tattalin arzikin Gwamnati, ba za mu iya yi mukadai ba” a cewar shi.
A karshe Jili, ya kuma yi kira da mutane dake zaune a kusa da rafuka a jihar, da su kaurace wa yankunan na tsawon wata guda ko biyu, domin kare kansu.
Idan za’a iya tuna wa dai, jihar Kano na daya daga cikin jihohin da hukumar NiMet ta bayyana cewa, da yuwar samun ambaliyar bana a jihar.