Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta shawarci wadansu yankuna guda hudu dake jihar Imo akan da su bar inda suke zuwa wuraren da za su tsira da rayukansu sakamakon barazanar ambaliyar ruwa wanda zai iya aukuwa a kowanne lokaci daga yanzu.
Yankuna hudun sun hada da; Eziorsu, Afiaofu, Orsuobodo da Ossemotto dake kananan hukumomin Ohaji/Egbema da Oguta.
Shugaban hukumar NEMA din na yankin Imo/Abia, Evan Ugoh shi ne ya bukaci hakan a ranar Lahadi a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
Har wala yau, Ugoh ya ce al’ummar dake yankin kogunan Orashi bank da River Niger ambaliyar na iya shafarsu.