Kungiyar ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje wato NIDO reshen kasar Singapore sun yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zama masu kishin kasa musamman wajen ba da labarin Nijeriya, inda suka ce ta hakan ne yara kanana masu tasowa za su taso da kishin kasa.
Mataimakin kungiyar, Dr. Jonathan Obaje shi ne ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da manema labarai.
Obaje ya yi wannan kiran ne a yayin da yake tsokaci dangane da bikin tunawa da ranar ‘yancin kai da zai gudana a ranar 1 ga watan Oktoba, wanda Nijeriya ta cika shekara 59 da samun ‘yancin kai.
Ya karfafi bayyanawa kananan yara labarai kan kasa da kuma wadansu daidaiku da kungiyoyi da suka sadaukar wajen ci gaban kasarnan, wanda suka ce hakan zai karfafe su wajen bunkasa kishin kasar su.